Kotu Ta Tabbatar da Hukuncin Daurin Farfesan da Ya Taimakawa Akpabio Murde Zabe
- Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Peter Ogban saboda magudin zabe da ya yi don Godswill Akpabio
- An zargi Farfesa Ogban da sauya sakamakon zabe a kananan hukumomi biyu domin bai wa jam’iyyar APC nasara a kan PDP
- Kotun ta yi Allah-wadai da halin Farfesan na jami'ar UNICAL a matsayin malami da ya shiga harkar magudin zabe a kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kotun daukaka kara da ke Kalaba ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Farfesa Peter Ogban, wanda aka daure a 2021 bisa yiwa Godswill Akpabio magudin zabe.
An zargi Farfesa Ogban da magudin zabe a zaɓen Sanata da aka yi don Godswill Akpabio, Sanatan daga jihar Akwa Ibom.

Asali: Facebook
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa magudin zaben ya faru ne a lokacin da Akpabio ya fadi zaben, kafin ya sake tsayawa takara a 2023 da ya samu nasara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka daure Farfesa saboda magudin zabe
Leadership News ta wallafa cewa an daure Farfesa Ogban, wanda ke aiki a jami'ar Kalaba, na tsawon shekara uku bayan hukuncin kotun dake zama a jihar Akwa Ibom.
An zarge shi da sanar da sakamakon zabe na bogi a cikin kananan hukumomi biyu – Oruk Anam da Etim Ekpo saboda Sanata Akpabio ya yi nasara.
Lauya daya daga cikin wadanda suka shiga shari'ar a kotun daukaka kara a ranar Laraba ya ce kotun ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Ogban na daurin shekara uku.
Haka kuma, kotun ta nuna rashin jin daɗi game da rawar da Farfesa Ogban ya taka a matsayin malami na jami'a wajen shirya magudin zaben.
Kotun daukaka kara ta tabbatar hukuncin dauri
Rahoton da ci gaba da cewa tsohon babban jami’i a Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), wanda ke da masaniya a kan lamarin, ya tabbatar da hukuncin.
Da fari, Farfesa Ogban ya shaida wa kotun tarayya a Uyo yadda aka canza sakamakon zabe domin bai wa jam’iyyar APC damar lashe zabe.
Dan takarar PDP, Chris Ekpenyong, wanda ya taba zama mataimakin gwamnan jihar Akwa Ibom, ya doke Akpabio a zaben da aka samu tashin hankali.

Asali: Facebook
Kafin a yanke masa hukunci, Farfesa Ogban ya roki kotu da ta yi masa sassauci, amma Mai Shari'a Augustine Odokwo ya ce dole doka ta yi aikinta.
Ya bayyana cewa shaidu sun tabbatar da cewa an yi magudin zabe, kuma an shigar da kara a kan Ogban bisa hujja mai karfi.
Leadership ta ce Akpabio ya dage cewa bai da hannu a zargin yin murdiya a zaben kujerar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso yamma.
Akpabio ya kalubalanci hukuncin kotu
A baya, mun wallafa cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya kalubalanci ikon Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja wajen sauraron karar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanatar daga Kogi ta Tsakiya ta shigar da kara a kotu tana kalubalantar matakin ladabtar da ita da Majalisar Dattawa ta dauka saboda matsalar da ta samu da shugaban majalisa.
Tawagar lauyoyin Godswill Akpabio karkashin jagorancin Kehinde Ogunwumiju, SAN, sun kalubalanci ikon kotun na tsoma baki a harkokin majalisa dake da 'yancinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng