An Gargadi Mutane bayan Rade Radin Tinubu Ya Kori Matawalle daga Muƙaminsa
- Wata ƙungiya mai suna 'Guardians of One Nigeria' ta gargadi masu yaɗa jita-jita da ka da su dagula ayyukan karamin ministan tsaro, Bello Matawalle
- Ƙungiyar ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa an sallami Matawalle da wasu Ministoci, tana mai cewa hakan yaudara ce da ke cutar da ƙasa
- Ta bayyana cewa Matawalle ya fi waɗanda suka riga shi ƙoƙari, kuma yana ziyartar dakarun da ke bakin daga domin ƙarfafa musu guiwa
- Ƙungiyar ta ce tsaro ba aikin mutum ɗaya ba ne, kuma ya kamata ‘yan siyasa su daina amfani da shi don cimma muradunsu na siyasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ƙungiyar 'Guardians of One Nigeria (GON)' ta yi gargadi kan matsawa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Kungiyar ta gargadi mutane da su daina ƙoƙarin dagula aikinsa da neman kawar da hankalin Matawalle.

Asali: Twitter
An ƙaryata labarin korar Matawalle daga mukaminsa
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugabanta, Darius Ishakwu ya fitar a Abuja, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta yi Allah-wadai da labarin da ake yaɗawa cewa an sallami ministan tsaro, Matawalle daga mukaminsa.
GON na martani ne ga jita-jitar da ta karade kafafen sada zumunta cewa a ranar Talata shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya sallami wasu ministoci uku.
Labarin ya ce an sallami su ne saboda gazawarsu wajen dakatar da kashe-kashen da ake ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya a sassan ƙasar.

Asali: Facebook
Matawalle: An gargadi mutane kan yaɗa karya
Ƙungiyar ta shawarci masu yaɗa irin wannan ƙarya da su daina, tana mai cewa Matawalle ya fi wanda suka riga shi zama a kujerar nasara wajen yaƙi da ta’addanci.
Sanarwar ta ce:
“Ina da tabbacin cewa da tsofaffin ministocin tsaro sun yi rabin abin da Matawalle ya yi, da ba za mu rika maganar rashin tsaro haka ba.
“Siffofin bajinta da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ke nunawa a fagen yaƙi, na nuni da haɗin kai tsakanin manyan hafsoshin tsaro.
“Jiya da aka bazama da labarin ƙarya a intanet, Matawalle da Janar Musa sun ziyarci dakarun yakin a Borno domin karfafa musu guiwa.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa akwai hujjoji da ke nuna cewa Matawalle yana ziyartar dakarun da ke fagen fama da ‘yan ta’adda a sassa daban-daban.
Ta ce Matawalle ya san aikinsa kuma bai kamata a dame shi ba inda ta ce za ta ci gaba da goyon bayansa har sai ya kawo karshen ‘yan ta’adda.
Tinubu ya musanta korar Bello Matawalle
Kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta musanta labarin cewa an kori Ministan tsaro da Karamin Minista a ma'aikatar da na makamashi daga mukamansu.
Hadimin shugaban kasa a bangaren yada labarai, Bayo Onanuga ya bayyana cewa labarin da ke yawo ba shi da tushe bare makama.
Onanuga ya roki jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa a kan shafukan da ke yada labaran karya ba tare da wani bincike ba.
Asali: Legit.ng