Yaki da Iran: An Gano Amurka na Fuskantar Barazanar Karancin Makamai

Yaki da Iran: An Gano Amurka na Fuskantar Barazanar Karancin Makamai

  • Rahotanni sun nuna cewa Amurka za ta fuskanci hadarin karancin makamai masu linzami idan wani sabon yaki ya barke da Iran bayan tsagaita wuta
  • An samu bayanai game da hakan ne duk da yadda shugaban kasa Donald Trump ya rika ikirarin cewa Amurka na da dimbin makamai a ajiye
  • Wani rahoto ya nuna cewa Amurka ta fara shirin kara adadin makamai masu linzami, sai dai an ce za a iya daukar shekaru kafin cike gurbin da aka samu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Amurka ta karar da dama daga rumbun ajiyar muhimman makamai masu linzami a yayin yakin da ta yi da Iran.

An bayyana cewa lamarin ya haifar da fargabar iya karewar makamai idan wani sabon rikici ya taso cikin ‘yan shekaru masu zuwa.

Kara karanta wannan

Amurka ta farmaki jirgin Iran a teku, China ta fitar da gargadi ga Trump

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

CNN ta wallafa cewa masana da wasu mutane uku da ke da masaniya kan sababbin bayanai game da ma’aikatar tsaron kasar ne suka sanar da ita.

Yadda Amurka ta karar da makamai

A cikin mako bakwai na yaki da Iran, rundunar sojin Amurka ta karar a kalla kashi 45 cikin 100 na makamai masu linzami a rumbun ajiyarta.

Rahoto ya nuna cewa ta karar da kalla rabin makamai na THAAD, wadanda ake amfani da su wajen dakile makamai masu linzami.

Haka kuma ta karar da kusan kashi 50 cikin 100 na makaman kariya na Patriot, kamar yadda wani sabon bincike ya nuna.

Rahoton Jerussalem Post ya nuna cewa wadannan alkaluma sun yi daidai da bayanan sirri na Pentagon kan ajiyar makaman Amurka.

Kokarin habaka makaman Amurka

Wani bincike ya nuna cewa a farkon wannan shekarar, Pentagon ya rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi domin kara samar da wadannan makamai da aka karar.

Kara karanta wannan

Iran ta yi wa Amurka da Isra'ila illa, ta tarwatsa 'yan leken asirinsu

Amma duk da haka, masana da majiyoyi sun ce zai dauki tsakanin shekaru uku zuwa biyar kafin a maye gurbin su duk da karin karfin samarwa.

Ana ganin Amurka na da isassun bama-bamai da makamai masu linzami da za su ci gaba da yakar Iran idan yarjejeniyar tsagaita wuta ta rushe, amma na gajeren lokaci.

Wani bincike ya ce adadin makaman da suka rage ba zai wadatar ba wajen fuskantar babbar kasa mai karfi kamar China, kuma zai dauki shekaru kafin a dawo da rumbun ajiyar zuwa matakin da yake kafin yakin.

Wasu makamai da Amurka ta karar

Rahoton ya kuma nuna cewa Amurka ta kashe kusan kashi 30 cikin 100 na makaman Tomahawk; sama da kashi 20 cikin 100 na makaman JASSM masu nisa; da kusan kashi 20 cikin 100 na makaman SM-3 da SM-6.

Rahotanni sun bayyana cewa ana sa ran zai dauki kusan shekaru hudu zuwa biyar kafin Amurka ta samu damar maye gurbin makaman.

Wani jirgin yakin Amurka
Daya daga cikin jiragen yakin Amurka a tekun Japan. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ba za a cigaba da yakin Iran ba

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa ba za a cigaba da yaki da Iran ba idan wa'adin tsagaita wuta ya kare.

Kara karanta wannan

Ana maganar sulhu, Trump ya yi barazanar sake sakin bama bamai a Iran

Ya bayyana haka ne yayin da wa'adin zai kare a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilun 2026 duk da kauracewa zama a Pakistan da Iran ta yi.

Firaministan Pakistan ya yaba da matakin da Trump ya dauka, inda ya yi kira a bangarorin da su girmama yarjejeniyar domin samar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng