2027: Shugaba Tinubu Ya Ci Gaba da Sukar 'Yan Adawa, Ya Bayyana 'Yaudarar' da Suke Yi

2027: Shugaba Tinubu Ya Ci Gaba da Sukar 'Yan Adawa, Ya Bayyana 'Yaudarar' da Suke Yi

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake yin suka mai zafi kan 'yan adawa yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027
  • Mai girma Bola Tinubu ya caccaki 'yan adawa, inda ya zarge su da kin yarda da abubuwan da suke magana a kai
  • Shugaban kasar ya kuma soki matakan da gwamnatocin baya suka dauka musamman a fannin samar da wutar lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - A lokacin da ake sauraron buga gangar siyasa, Shugaban kasa Bola Tinubu ya kakkausar suka kan ‘yan siyasar adawa a Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu wanda yake kan karagar mulki tun 2023 ya zarge su da raunana dabi’un dimokuradiyya yayin da suke ikirarin kare su.

Shugaba Tinubu ya soki 'yan adawa
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Bola Tinubu ya karbi bakuncin 'yan siyasa

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Ministan makamashi na shirin ajiye aiki, zai shiga takarar gwamna a 2027

Tinubu ya yi magana ne a ranar Talata, 21 ga watan Afilun 2026 lokacin da ya karbi bakuncin tawagar shugabannin siyasa daga jihar Enugu, karkashin jagorancin Gwamna Peter Mbah, a fadar Aso Rock dake Abuja.

Fatan Tinubu kan dimokuradiyya a Najeriya

Yayin da yake jawabi ga tawagar, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa dimokuradiyya za ta dore a Najeriya duk da abin da ya kira tsoratarwa.

“Dimokuradiyya za ta rayu, duk da dukkan tsoratarwa. Ku yi watsi da ita, kamar yadda nake ba kaina shawara; ku mayar da hankali. Idan kuna samun nasara su kuma suna fushi, ku kyale su da halinsu."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya kuma soki matakan da gwamnatocin baya suka dauka, musamman a bangaren wutar lantarki, inda ya jaddada bukatar mayar da hankali kan sake gina kasar.

Me Shugaba Tinubu ya ce kan 'yan adawa?

“Kuna da shugabannin da suka mayar da harkar wutar lantarki hannun ‘yan kasuwa wadda kuma ba ta aiki. Sun ba mu duhu, kamar yadda ku ka fada, kuma muna kokarin fitar da kanmu daga wannan domin gina kasa mai cike da kyakkyawan kwarin gwiwa da mutane masu farin ciki."

Kara karanta wannan

Sanata a ADC ya bukaci Atku ya hakura da takara, ya kawo dalili

“Amma su ko kadan ba su yarda da dimokuradiyyar da suke ta wa’azi a kanta ba. Kada ku saurare su domin ni ma ba na sauraren su."
“Muna tsayawa a kan turbar mu. Muna mayar da hankali. Muna gina rayuwarmu ne a kan mutane, walwala, arziki, da alkawarin yau da gobe.”

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya gana da 'yan siyasa daga jihar Enugu
Shugaba Bola Tinubu na gaisawa da tawagar 'yan siyasa daga jihar Enugu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaban ya kara kare tsarin tattalin arziki da na gudanar da mulki na gwamnatinsa, inda ya jaddada bukatar tsare-tsare na dogon lokaci wajen bunkasa kasa.

An ja kunnen Tinubu kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa jmaligo a jam’iyyar APC, Sanata Abubakar Yusuf, ya yi kira da babbar murya ga Shugaba Bola Tinubu kan zaben 2027.

Sanata Abubakar Yusuf ya bukaci Shugaba Tinubu da kada ya dogara da goyon bayan gwamnonin jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Ya bayyana cewa idan har Tinubu ya sa rai da samun nasara saboda gwamnonin APC, za a iya samun matsala a zaben shugaban kasa da ke tafe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng