An Lissafo Ayyukan da Tinubu zai Bude a Katsina a Ziyarar da zai kai Jihar
- An sanar da cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki ta yini daya a jihar Katsina a ranar Juma’a mai zuwa
- A yayin ziyarar, Bola Tinubu zai kaddamar da manyan ayyuka biyu da gwamnatin Gwamna Dikko Radda ta aiwatar a jihar
- Kwamishinan yada labarai ya ce wannan ce ziyarar aiki ta farko da Tinubu zai kai Katsina tun bayan hawansa mulki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana shirin kai ziyarar aiki ta yini daya zuwa jihar Katsina a ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu, 2025.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Bola Tinubu zai kai ziyarar ne domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta kammala.

Asali: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa kwamishinan yada labarai na jihar, Dr Bala Salisu-Zango, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Laraba a Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya ce wannan ne karon farko da Shugaba Tinubu zai kai irin wannan ziyarar aiki jihar tun bayan hawansa mulkin Najeriya a watan Mayun 2023.
Ayyukan da Tinubu zai bude a jihar Katsina
Daga cikin ayyukan da shugaba Tinubu zai kaddamar akwai titin da ya taso daga Dutsin-ma, ya ratsa ta titin Kano/Daura, har ya kare a Yandaki da ke karamar hukumar Kaita.
Kwamishinan labarai, Salisu-Zango ya ce titin na da matukar amfani wajen saukaka zirga-zirgar abubuwan hawa, musamman ga mazauna yankin da masu zuwa jihar daga wasu sassa.
Haka zalika, Tinubu zai kaddamar da Cibiyar Noma ta zamani (Agricultural Mechanisation Centre) da aka gina a jihar domin bunkasa harkokin noma da amfani da na’urorin zamani.
Ziyarar za ta bude kofar tattaunawa da Tinubu
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi tanadin amfani da wannan ziyara wajen gabatar da matsalolin tsaro da sauran kalubale da al’ummar jihar ke fuskanta ga shugaban kasa.

Asali: Twitter
Dr Bala Salisu-Zango ya ce:
“Ziyarar ba wai kawai kaddamar da ayyuka ba ce, har ila yau dama ce da gwamnatin jihar za ta gabatar da bukatun al’umma kai tsaye ga Shugaba Tinubu.”
PM News ta wallafa cewa Salisu-Zango ya yi kira ga al’ummar Katsina da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tarbar shugaban kasa tare da nuna halin kirki da biyayya ga doka da oda.
Ana sa ran mutanen jihar Katsina za su nuna karamci da hakuri a yayin wannan ziyara domin tabbatar da bude ayyukan lami lafiya.
'Yan bindiga sun mika wuya a jihar Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da suka addabi al'umma sun mika wuya a jihar Katsina.
Rahotanni sun cewa daga cikin manyan 'yan ta'addan da suka mika wuya akwai Umar Black da ya shahara da satar mutane da kai hari.
An kafa sharudan karbar tuban 'yan bindigar, kuma su ma sun bukaci gwamnati ta musu adalci musamman wajen inganta rayuwarsu.
Asali: Legit.ng