"Na Amsa Kiran Shugabana," Ɗan Majalisar Dokoki Ya Yi Murabus daga Kujerarsa

"Na Amsa Kiran Shugabana," Ɗan Majalisar Dokoki Ya Yi Murabus daga Kujerarsa

  • Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Karim-Lamiɗo II a Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Hon. Mike Dio Jen ya yi murabus daga kujerarsa
  • Hone Mike Jen ya ajiye kujerarsa ta ɗan Majalisa ne domin karɓar muƙamin kwamishinan kula da harkokin manyan makarantun Taraba
  • Ya bayyana Gwamna Agbu Kefas a matsayin ubangidansa na siyasa wanda duk abin da ya umarce shi ya yi, zai aikata ba tare da ɓata lokaci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taraba - Dan majalisar dokokin jihar Taraba mai wakiltar mazabar Karim-Lamido II, Hon. Mike Dio Jen, ya yi murabus daga matsayinsa na zaɓaɓɓen mamban Majalisa.

Hon. Mike ya ajiye muƙaminsa na ɗan Majalisa mai wakiltar Karim-Lamiɗo II ne domin karɓar muƙamin kwamishina da Gwamna Agbu Kefas ya ba shi.

Hon. Mike Jen.
Dan Majalisar Dokokin Taraba ya yi murabus don karbar mukamin kwamishina Hoto: Auwal Abdullahi
Asali: Facebook

Ɗan Majalisa ya yi murabus a Taraba

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Gwamna Kefas na jihar Taraba ya naɗa Mike Dio Jen a matsayin sabon kwamishinan kula da harkokin manyan makarantu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mike Jen ya bayyana aniyarsa ta sauka daga kujerar ‘dan majalisa ne jim kaɗan bayan Gwamna Agbu Kefas ya naɗa shi a wannan matsayi na kwamishina.

Sakataren Gwamnatin Jihar Taraba, Barista Gibson Kataps, ne ya sanar da naɗin Mike Jen a wata sanarwa da ya fitar a ranar 15 ga Afrilu, 2025.

Me yasa ɗan Majalisar ya ajiye kujerarsa?

Da yake magana, Hon. Jen ya ce a shirye yake ya ya sauka daga kujerar majalisar domin yin biyayya ga umarnin Gwamna Kefas wanda ya kira "ubangidansa na siyasa."

“Al'ummar mazaɓata sun nuna damuwa da farin ciki da wannan mukami da aka ba ni na Kwamishinan Ma’aikatar Manyan Makarantu.
“Gwamna, Dakta Agbu Kefas shi ne shugabanmu, duk abin da ya ce in yi, zan yi. Ko ya ce na je na zama Kansila a gundumata a Karim-Lamido, zan je.

“Idan Gwamna ya ga wani alheri a tattare da ni, kuma ya nemi na taho na taimake shi a wannan bangare, ba zan yi wata-wata ba zan amsa kira."

- Hon. Mike Jen.

Gwamna Kefas.
Dan Majalisa ya karɓi mukamin kwamishina a Taraba Hoto: Agbu Kefas
Asali: Twitter

Hon. Mike Jen ya karɓi muƙamin kwamishina

Hon. Mike ya ƙara da bayyana farin cikinsa bisa wannan muƙami tare da karbarsa hannu bibbiyu domin ci gaban jihar Taraba.

“Don haka, ina murna da hakan, kuma ina rokon mutane su fahimci cewa a kowace kasa ko ma’aikata, akwai shugaba. Ni kuma ina bin abin da shugabana ya ce in yi masa.
“Zan ajiye kujerar wakilcin mazabar Karim-Lamido II a Majalisar Dokokin Taraba domin a shirya zaɓen cike gurbi wanda wani zai fito ya maye gurbina,” in ji shi.

Gwamnan Taraba ya naɗa masu HIV a muƙami

A baya, kun ji cewa Gwamna Agbu Kefas na Taraba ya naɗa wasu mata biyu a muƙaman gwamnati bisa faɗin gaskiya kan cutar kanjamau da suke ɗauke da ita.

Gwamna Kefas ya ce gwamnatinsa za ta bai wa matan su biyu aiki na musamman bayan sun tabbatar da cewa suna ɗauke da cutar tsawon shekaru 10.

Tun farko dai matan sun bayyana ƙalubalen da suka fuskanta bayan kamuwa da cutar a taron jama'a ba tare da tsoro ko jin kunya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262