Ana Wata ga Wata: Matashi Ya Ƙi Karbar babban Muƙami da Gwamnan Bauchi Ya ba Shi

Ana Wata ga Wata: Matashi Ya Ƙi Karbar babban Muƙami da Gwamnan Bauchi Ya ba Shi

  • Malam Musa Ahmad Azare ya ki karbar nadin da gwamnan Bauchi ya yi masa matsayin mataimaki na musamman kan siyasa da al'umma
  • Azare na daga cikin sababbin hadimai 168 da Gwamna Bala Muhammad ya nada da nufin karfafa aikin gwamnati da yi wa al'umma hidima
  • A cikin wata wasika da ya aike wa gwamnan ta hannun sakataren gwamnati, Musa Azare ya bayyana dalilinsa na kin karbar wannan babban tayi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Wani matashi, Malam Musa Ahmad Azare ya ki amincewa da nadin da gwamnatin Bauchi ta yi masa a matsayin babban mataimaki ga gwamna kan siyasa da al’umma.

A wata wasika da ya rubuta wa Gwamna Bala Mohammed ta hannun sakataren gwamnatin jiha, Musa Azare ya gode wa gwamnati bisa wannan karamci, amma ya ce ba zai karbi tayin ba.

Musa Azare ya ki karbar mukamin SSA da gwamnan Bauchi ya ba shi.
Wasikar da Musa Azare ya aika wa gwamnan Bauchi kan kin karbar mukamin SSA da aka ba shi. Hoto: Musa Azare
Asali: Facebook

Gwamnan Bauchi ya nada sababbin hadimai 168

Musa Azare, a cikin wasikar da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 30 ga Afrilu, ya shaida cewa gwamnan Bauchi cewa zai koma aikin shari'a maimakon zama hadiminsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dai na zuwa ne 'yan awanni da gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya nada sabbin hadimai 168 domin ƙarfafa harkokin mulki a fadin jihar.

Mun ruwaito cewa, mai magana da yawun Gwamna Bala, Mukhtar Gidado, ya ce an yi sababbin nade-naden ne domin kusanto da jama'a ga ayyukan gwmanati.

Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai masu mukamin PSA 7, da kuma SSA 61. Haka kuma, gwamnan ya naɗa SA guda 38 da PA guda 63.

Matashi ya ki karbar mukamin SSA a Bauchi

To sai dai, a yayin da wadanda suka samu mukaman ke murna, a hannu daya, Musa Azare ya ce ba zai iya karɓar nadin ba saboda bukatarsa ta cigaba da aikinsa a ma’aikatar shari’a.

A cikin wasikar da ya aika wa gwamnan, Musa Azare ya ce:

“Na gode matuka bisa wannan mukami da aka ba ni, amma bayan shawarwari da iyalai, makusanta da masoya, na yanke shawarar komawa aikina na asali a ma'aikatar shari'a ta tarayya."

Azare ya tunatar da gwamnan cewa a ranar 18 ga Yuli, 2019 ne aka buƙaci da ya shigo cikin harkokin gwamnatin jihar Bauchi domin ba da gudunmawarsa, kuma yanzu yana ganin dacewar ya koma inda ya baro.

An samu mutum 1 daga cikin 168 da yaki karbar mukamin da gwamnan Bauchi ya ba shi
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed tare da Malam Musa Azare. Hoto: Musa Azare
Asali: Facebook

Musa Azare ya yiwa gwamna fatan alheri

Ya ce duk da hakan, yana goyon bayan ci gaban da gwamnatin Bala Mohammed ke kawo wa a Bauchi, tare da yi mata fatan samun wasu nasarorin a gaba.

Musa Azare ya tabbatar da cewa shawarar da ya yanke ba ta da alaƙa da wata sabani da gwamnati ko wani ra’ayi na siyasa, sai dai tsantsar kishin aiki da kwarin guiwar cigaba da hidima.

Gwamnatin jihar Bauchi dai ta ce za ta ci gaba da yin aiki tare da ƙwararru da masu hangen nesa domin tabbatar da cewa kowa ya samu wakilci da dama a cikin tsarin mulki.

Karanta sanarwar Musa Azare a kasa:

Musa Azare ya fadi alherin marigayi Dutsen Tanshi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani ɗan siyasa daga Bauchi, Musa Azare, ya bayyana irin mawuyacin halin da Dr. Idris Dutsen Tanshi ya tsinci kansa a lokacin rashin lafiyarsa.

Azare ya ce lokacin da Sheikh Idris ya isa asibiti a ƙasar Indiya, likitoci sun ba da shawarar ya ci gaba da zama a can don karɓar magani yayin da za a shirye-shirya yi masa tiyata.

Amma Shehin ya ƙi amincewa da hakan, yana mai bayyana cewa ya fi son komawa Najeriya, domin in mutuwa ta zo, ta same shi cikin iyalinsa da ‘yan uwansa Musulmai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.