Tofa: Iran Ta Kai Sabon Hari da Zai Iya Rusa Shirin Tattaunawar Sulhu da Amurka

Tofa: Iran Ta Kai Sabon Hari da Zai Iya Rusa Shirin Tattaunawar Sulhu da Amurka

  • Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta harba harsasai kan wani jirgin dakon mai a yau Laraba, lamarin da ya ƙara dagula shirye-shiryen tattaunawar sulhu
  • Wannan hari ya zo ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya tsawaita wa'adin tsagaita wuta domin bai wa Iran damar gabatar da shawarwarin zaman lafiya
  • Mashigar tekun ta Hormuz, wadda kashi 20 na man fetur ɗin duniya ke bi ta cikinta, na ci gaba da kasancewa filin daga tun a ranar 28 ga Fabrairu 2026

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran – Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta ƙasar Iran ta kai hari kan wani jirgin dakon ai a mashigar tekun Hormuz a safiyar yau Laraba.

Wannan danyen aiki ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin sake tattara Amurka da Iran a ƙasar Pakistan domin tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙin da ake yi.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Sojojin Iran sun bude wuta kan wani jirgin dakon mai da ya shiga Hormuz
Wani jirgin dako, dauke da man Saudiyya ya kama da wuta bayan harin Iran a gabar tekun Dubai. Hoto: NORBERT SCHILLER/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Harin na safiyar yau ya faru ne sa'o'i kaɗan bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsawaita wa'adin tsagaita buɗe wuta ba tare da ƙayyadadden lokaci ba, in ji rahoton AP News.

Iran ta bude wa jirgi wuta a Hormuz

Trump ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin bai wa Tehran damar fito da "haɗaɗɗiyar shawara" kafin a fara tattaunawa a birnin Islamabad.

Kodayake hukumar lura da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta bayyana cewa dakarun Iran sun buɗe wuta ba tare da bayar da gargaɗi ba, Iran ta musanta hakan.

Iran ta yi ikirarin cewa jirgin ya yi kunnen uwar shegu da umarnin dakarun ƙasar ne, don haka suka buɗe masa wuta domin "tabbatar da ikonsu kan mashigar Hormuz."

NBC News ta rahoto cewa wannan hari na zuwa ne a matsayin martani ga matakin da Amurka ta ɗauka na ƙwace wani jirgin Iran a karshen mako, da kuma ci gaba da katange tashoshin jiragen ruwan Iran, matakin da Iran ta kira "abin da ba za a amince da shi ba."

Kara karanta wannan

Iran ta sabunta makamai yayin tsagaita wuta da Amurka, tana shirin ko ta kwana

Tasirin yaƙin ga tattalin arziƙin duniya

Tun bayan harin da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, wanda ya haddasa ɓallewar yaƙi, Iran ta taƙaita zirga-zirga a mashigar Hormuz.

Iran ta ce ta farmaki jirgin dakon mai a tekun Hormuz saboda ya bijire wa umarninta.
Wani jirgin dakon mai a mashigar ruwan Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wannan ya yi sanadiyyar tashin farashin man fetur a duniya inda ɗanyen mai ya kai dala $98 a ko wace ganga a yau, wanda hakan ke nuna ƙaruwar 30% tun farkon yaƙin.

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya godewa Trump kan tsawaita tsagaita wutar, inda ya bayyana cewa hakan zai ba da damar ƙarfafa diflomasiyya.

Sai dai harin da IRGC suka kai yau, da barazanar da suka yi na "kai munanan hare-hare," na iya rusa tattaunar sulhun da ake kokarin yi a Islamabad.

Iran ta farmaki jirage a Hormuz

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Rundunar dakarun Iran ta IRGC ta buɗe wa aƙalla jirgin ruwa ɗaya wuta a yankin tekun Oman a ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan

Iran ta nuna wa Trump yatsa, ta bude wuta kan wasu jirage da suka shiga Hormuz

Wannan mataki ya biyo bayan sake sanar da rufe mashigar Hormuz da Tehran ta yi, kamar yadda hukumar kula da harkokin kasuwancin teku ta Birtaniya (UKMTO) ta bayyana.

Jiragen yaƙi biyu na Iran sun bi sahun wani jirgin dakon mai, daga tazarar mil 20 da gabar tekun Oman, inda suka buɗe wa jirgin wuta ba tare da wani gargadi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com