Gwamnatin Kano Ta Kinkimo Manyan Ayyuka, Abba Ya Ware Masu N50bn
- Majalisar zartarwar Kano ta amince da fitar da Naira biliyan 51.5 domin kara wadata jihar da abubuwan more rayuwa a sassa da dama
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ba da izinin gudanar da muhimman ayyuka, da suka hada da gyaran tituna da shigar da sabunta ma'aikata
- Majalisar ta amince a ware Naira biliyan 5.4 don gyaran tituna daga gidan Mumbayya zuwa kwanar Tal’udu da wasu titunan a Kano
- Gwamnatin NNPP ta kuma amince da yin amfani da Naira biliyan 1.46 don sabunta Ma’aikatar Wutar Lantarki dake Sharada a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Majalisar Zartarwar jihar Kano ta amince da Naira biliyan 51.5 don gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa a fadin jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan yana daga cikin aniyarta na inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewa al'ummar jihar.

Asali: Facebook
Darakta Janar a kan yada labaran gwamnatin Kano, Sunusi Dawakin-Tofa, ne ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta dauko manyan ayyuka
Jaridar Leadership News ta ruwaito cewa majalisar ta ba da izinin fara wasu muhimman ayyuka, ciki har da gyaran manyan tituna.
Sauran ayyukan sun hada da shigar fadada gine-ginen gwamnati, da sabunta tsarin samar da wutar lantarki domin inganta rayuwar mazauna jihar.

Asali: Facebook
Daga cikin kudin da aka amince a fitar, akwai Naira biliyan 5.4 don gyaran tituna da shimfida kwalta daga gidan Mumbayya zuwa kwanar Tal’udu, Gadon Kaya, titin Yahaya Gusau Road, da na Sharada.
An kuma ware Naira biliyan 3.4 don samar da wutar danja masu amfani da hasken rana a birnin Kano a karkashin Shirin Sabon Ci gaban Birane.
Gwamnatin jihar Kano za ta gina hanyoyi
Sanarwar ta ce an amince da fitar da wasu kudi don gina sababbin hanyoyi daga titin Miller zuwa na Mission, da kuma gyaran wasu muhimman gine-ginen gwamnati.
Majalisar ta kuma amince da fitar da Naira biliyan 1.46 don sabunta Ma’aikatar Wutar Lantarki da da ke cikin Sharada Phase I Industrial Layout.
Sanarwar ta ce:
"Amincewa da fitar da wannan kudi yana nuna jajircewar gwamnatin wajen ci gaba mai dorewa a fannin bunkasa birane da kuma inganta hidimar jama’a."
Gwamnatin Kano za ta biya kansiloli hakkinsu
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ta amince da fitar da N15.6bn domin biyan kudin fansho da sauran hakkokin tsofaffin kansiloli guda 3,000 daga kananan hukumomi 44 na jihar.
Sanarwar da Ibrahim Adam, mai ba gwamna shawara kan harkokin yada labarai, ya fitar ta ce wannan mataki yana daga cikin kokarin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na sauke nauyin aikinsa.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa za a raba kudin a cikin kashi uku, kuma biyan zai fara a cikin Afrilu, Mayu, da Yuni na shekarar 2025, domin saukaka nauyin da ke kan gwamnati da ta gada.
Asali: Legit.ng