Kasashen Larabawa Sun Shiga Uku, Kasar Iran Ta Yi Masu Gagarumin Barazana
- Wani babban kwamandan sojin Iran ya gargadi ga kasashen Larabawa makwabta kan rikici a yankin Gabas ta Tsakiya
- Janar Majid Mousavi ya yi gargadin cewa masana’antun man fetur a yankin Gulf na iya cin karo da matsala idan rikici ya sake ɓarkewa
- Mousavi ya ce duk wata ƙasa da ta ba Amurka damar amfani da ƙasarta wajen kai hari kan Iran, za ta iya fuskantar mummunan sakamako
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Wani babban kwamandan Iran, Janar Majid Mousavi, ya yi gargadi ga kasashen Labarawa kan rikicin da ke faruwa.
Mousavi ya bayyana cewa masana’antun man fetur a yankin Gulf na iya cikin hadari idan rikici ya sake ɓarkewa a yankin.

Source: Getty Images
Rahoton Al Jazeera ya bayyana cewa Mousavi ya yi wannan gargadi ne kai tsaye ga kasashen yayin da ake ci gaba da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
"Abu 1 muke tsoro," Qatar ta tsoma baki kan batun tattaunawar sulhun Amurka da Iran
Matsalar da aka samu a sulhun Iran da Amurka
Duka wannan rigima ta biyo bayan rugujewar sulhu da aka shirya tsakanin Iran da Amurka a kasar Pakistan domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Hakan a biyo bayan shafe kusan wata biyu ana bata kashi tsakanin Iran da Isra'ila wacce ke samun goyon bayan Amurka.
An fara kai harin ne a ranar Asabar 28 ga watan Faburairun shekarar 2026 a birnin Tehran wanda ya yi ajalin manyan jami'an tsaro.
Yayin harin, jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya rasa ransa da wasu manyan jami'an tsaron kasar wanda ya yi gagarumar illa ga Jamhuriyar Musulunci.
Daga bisani, kasar ta fusata inda ta fara kai hare-haren ramuwar gayya kan Isra'ila da Amurka har ma da kasashen Larabawa da suka ba sojojin Amurka mafaka.

Source: Getty Images
Gargadin da Iran ta yi ga kasashe makwabtanta
Mousavi, wanda ke shugabantar sashen sararin samaniya na rundunar IRGC, ya ce duk wani sabon hari da za a kai wa Iran babban kuskure ne.
Ya bayyana cewa idan ƙasashen yankin suka ba Amurka damar amfani da ƙasashensu wajen kai hari kan Iran, za su iya fuskantar martani mai tsanani.
A cewarsa, cibiyoyin man fetur a yankin Gulf na iya lalacewa matuƙa idan aka samu irin wannan goyon baya ga ayyukan sojin Amurka, cewar rahoton India Today.
“Idan maƙwabta suka bari aka yi amfani da cibiyoyinsu wajen kai hari kan Iran, su yi bankwana da samar da mai a yankin Gabas ta Tsakiya.”
- In ji Mousavi.
Saudiyya ta sallami jami'an Diflomasiyyar Iran
Mun ba ku labarin cewa kasar Saudiyya ta sallami wasu daga cikin jami’an diflomasiyyar Iran biyar tare da ba su awa 24 su fice daga kasar.
Matakin ya biyo bayan hare-haren jiragen sama marasa matuki da makamai da ake zargin Iran na kai wa cibiyoyin mai da fararen hula.
Rikicin Amurka, Isra'ila da Iran ya kara dagula yankin tare da tasiri kan kasuwar makamashi ta duniya wanda ya jawo matsala ga tattalin arzikin duniya a halin yanzu.
Asali: Legit.ng
