Latest
Mutane hudu masu ta'adar garkuwa da mutane sun yi gamo da fushin hukumar tsaro yayin da jami'an 'yan sanda suka salwantar da rayukan su a karamar hukumar Bali ta jihar Taraba dake Arewa maso Gabashin Najeriya.
Tsautsayi gami da bacin rana sun auku a jihar Kogi yayin da wani karamin ma'aikacin soja Kofura Moses, ya sokawa wani direban mota Ogbimi wuka a ciki wanda yayi sanadiyar mutuwar sa nan take a sakamakon wata 'yar sa'insa.
Rahotanni sun kawo cewa a safiyar ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli wasu yan bindiga, sun kashe wani fitaccen dan kasuwa a garin Gulma da ke jihar Kebbi, Alhaji Usuf Garkar-Bore sannan suka yi garkuwa da surukarsa, Aisha.
Kasar Saudiya a ranar Litinin ta dugunzuma cikin shirye-shiryen gudanar da jana'izar 'dan uwa na jini da ya kasance babban Yaya ga Sarki Salman, wanda ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 96.
Idan aka ce Hepatitis, toh ana nufin ciwon Hanta kenan a Hausance. Hepatitis kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E.
Kimanin rayukan mutane 7 ne suka salwanta yayin da wani mummunan hatsarin mota ya auku a a kan wata babbar hanya a kauyen Kwalande dake karamar hukumar Maigatari a jihar Jigawa dake Arewa maso Yammacin Najeriya.
Kwanan nan ne wata Kungiya ta caccaki Iran bayan ta nemi a saki Zakzaky. Wannan Kungiya ta gargadi Gwamnatin Najeriya ta bi a hankali da Iran a kan shiga sharo ba shanun da ta ke wa kasar.
Kazalika cibiyar kula da harkokin ziyarce-ziyarce a aikin Hajji da Umara, a ranar Lahadi ta kaddamar da shirin fara jigilar maniyyatan wasu zababbun kasashe zuwa wurare na tarihi a birnin Madinah.
Ramatu ta kasance tana sana’ar sayar da charbin malam (alawar gargajiya), inda ta bayyana cewa tana samun naira miliyan daya da dubu dari hudu a kowani mako daa cikin wannan sana’a tata.
Masu zafi
Samu kari