Har yanzu akwai harsasai cikin jikin Zakzaky da matarsa - Femi Falana

Har yanzu akwai harsasai cikin jikin Zakzaky da matarsa - Femi Falana

Lauyan kungiyar yan Shi'a IMN, Femi Falana SAN ya bayyanawa manema labarai bayan zaman kotun yau cewa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zinat na bukatan kulawan asibiti cikin gaggawa saboda basu samu isasshen kula ba tun shekarar 2015.

Ya bayyana cewa har yanzu akwai barbashin harsasai cikin jikin Sheikh Zakzaky da matarsa tun abinda ya faru a watan Disamban 2015 a Zaria.

Yayinda yake bayani kan halin da Zakzaky ke ciki, Falana yace Zakzay ya rasa idonsa daya kuma ya zama wajibi ya fita kasar waje da wuri.

A cewarsa: "Ya gaza zuwa kotu a yau saboda rashin lafiyarshi yayi tsanani. A zuwan kotun karshe da yayi, ya gaza hawa matakalan shiga kotu. Shi yasa muka bada hakurin cewa ba zai iya zuwa kotu ba kuma kotu ta bamu dama."

"Barbashin harsashin da ke jikinsu ya sanya musu guban karfe kuma ana bukatar kwararrun likitoci su ciresu."

Lauya Femi Falana ya bayyana cewa yanada imani kotu zata basu daman fita kasar waje.

A jawabin lauyan gwamnati, Dari Bayero, ya ce lauyoyin gwamnati sun duba takardun asibiti takwas da likitocin Najeriya da kasar waje suka gabatar, sun fahimci cewa akwai kayayyakin kiwon lafiya da za'a iya amfani da su wajen jinyan shugaban yan Shi'an da matarsa a Najeriya.

Babbar kotun jihar Kaduna ta daga karar bukatar fita jinya kasar wajen shugaban kungiyar IMN wanda akafi sani da yan Shi'a da uwargidarsa, Zeenat Zakzaky, zuwa ranar 5 ga watan Agusta, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel