Aikin Hajji: Maniyyatan Najeriya 24,993 daga jihohi 21 sun isa kasar Saudiya
Maniyyatan Najeriya daga jihohi 21 sun isa kasa mai tsarki domin sauke faralin aikin hajji na bana a yayin da kimanin jiragen sama 15 suka gudanar da aikin jigilarsu.
A ranar Lahadin da ta gabata, adadin maniyyatan Najeriya daga jihohi 21 da suka isa daular Larabawan sun kimanin 24,993 daja jihohin Kano, Legas, Abuja, Bauchi, Yobe, Taraba, Oyo, Osun, Ogun, Gombe, Katsina, Nasarawa, Kaduna, Kebbi, Kwara, Kogi, Sakkwato, Adamawa, Neja, Edo, da kuma Zamfara.
Kazalika cibiyar kula da harkokin ziyarce-ziyarce a aikin Hajji da Umara, a ranar Lahadi ta kaddamar da shirin fara jigilar maniyyatan wasu zababbun kasashe zuwa wurare na tarihi a birnin Madinah.
Kasashe shida da maniyyatansu zasu ci moriyar wannan shiri sun hadar da na Najeriya, Brunei, Thailand, Philippine, India da kuma Lebanon.
KARANTA KUMA: Rukunan mutane 13 da ya kamata a yiwa allurar riga kafin ciwon hanta
Jagoran wannan cibiya, Dr Ahmad Al-Shaabi, ya ce za yi jigilar maniyyatan kasashen shida zuwa wurare na tarihi masu nasaba da fiyayyen halitta, Manzon Tsira Muhammadu dan Abdullahi, tsira da Aminci Allah su kara tabbata a gare shi.
Wadansu daga cikin wuraren ziyara sun hadar da yankin Usba dake birnin Madinah, Wadi Mubarak Masallacin Quba, Jannatun Baqi, Dutsen Uhud, rijiyar Ghar, dausayi da kuma lambun daya daga cikin sahabbai, Salman Al Faris.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng