'Yan Bindiga Sun Farmaki 'Yan Sanda a Kwara, an Samu Asarar Rayuka
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wani sansanin 'yan sanda a jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka jami'an 'yan sanda tare da raunata wasu yayin harin wanda suka kai da safe
- Kwamoshinan 'yan sandan jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa jami'an da suka ji rauni na samun kulawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kwara - Wasu ’yan bindiga sun kai hari wani sansanin rundunar ƴan sanda masu kwantar da tarzoma (PMF) a jihar Kwara.
'Yan bindigan sun kai harin ne a yankin Tenebo, da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, inda suka kashe aƙalla jami’ai uku tare da raunata wasu guda biyu.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce harin, wanda ya faru a farkon sa’o’in ranar Asabar, 2 ga watan Mayun 2026, ya faru ne ba tare da jami’an tsaron sun yi tsammani ba.
'Yan bindiga sun farmaki sansanin 'yan sanda
An ce maharan sun afka wa sansanin ne da dambin yawa, inda wasu daga cikinsu suke kan babura yayin harin da suka kawo.
Wani mazaunin yankin, Mohammed Abdul, ya ce:
"Sun zo ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare da yawa kuma sun yi ƙoƙarin shiga garin amma jami’an tsaro suka nuna musu tirjiya, wanda hakan ya kai ga musayar wuta mai ƙarfi da aka shafe sa’o’i ana yi.”
“A ƙarshen artabun, an kashe jami’ai uku sannan biyu suka ji rauni. Ƴan bindigan sun bar wurin bayan hakan amma ba a yi garkuwa da kowa ba, kuma ba mu sani ba ko an samu asarar rai a ɓangarensu."
Mutane sun shiga firgici
Hakalika, wani mazaunin yankin, Halidu Umar, ya bayyana cewa:
“Babu wani daga cikinmu da yake da gidaje a wannan yankin da ya iya barci a daren jiya, kuma ko yanzu muna cikin tsoro domin yankin Tenebo kusan kilomita 4 ne kawai tsakaninsa da garin Kaiama."
“Yankin na Tenebo kuma shi ne ya nufi dajin nan na National Park inda waɗannan ’yan bindigan suke gudanar da ayyukansu. Kuma wannan lamari ya biyo bayan irin dabarunsu na baya inda za su zo su kai hari sannan su koma cikin daji."
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Jaridar TheCable ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Adekimi Ojo, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho.
"Haka ne, gaskiya ne kuma mun rasa jaruman jami’ai uku a harin, yayin da biyu suka ji rauni. Waɗanda suka ji raunin suna samun kulawa amma ba a kama kowa ba tukunna.”
- Adekimi Ojo

Source: Twitter
A watan da ya gabata, an samu makamancin wannan lamari inda ’yan bindiga suka mamaye wani sansanin haɗin gwiwa na jami’an tsaro a Kemanji, wani ƙauye da ke maƙwabtaka da Tenebo, inda suka kashe sojoji uku da jami’an 'yan sa-kai biyu.
Sun yi awon gaba da wata motar yaƙi ta sojoji da sauran kayan aiki a lokacin, amma su ma sun fuskanci asarar rayuka waɗanda suka tafi da su.
'Yan bindiga sun sace mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da mutane takwas a jihar Sokoto.
Wasu daga cikin wadanda suka fada hannun 'yan bindigan suna da alaka da mataimakin gwamnan jihar ta Sokoto, Idris Mohammed Gobir.
An ce ’yan bindigan sun shafe kusan awa biyu suna cin karensu babu babbaka a kauyen ba tare da wani daukin jami’an tsaro ba.
Asali: Legit.ng


