Italiya Ta Tsoma Baki kan Rigima a Mashigar Hormuz, Ta ba Iran Mafita kan Lamarin
- Ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani ya nuna damuwa kan karuwar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya yayin tattaunawa da takwaransa na Iran Abbas Araghchi
- Tajani ya bukaci kasashen duniya su kara kokarin diflomasiyya tare da bude mashigar Hormuz domin kaucewa matsalar abinci da rashin tsaro musamman a Afrika
- Italiya ta gargadi Iran kan shirin nukiliya na soja tare da bukatar amfani da tasirinta wajen dakatar da hare-haren Hezbollah kan Isra’ila da samar da zaman lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani ya tattauna da takwaransa na Iran a waya game da yakin da ake yi.
Tajani ya bayyana matukar damuwa kan yadda tashin hankali ke karuwa a Gabas ta Tsakiya wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Source: Getty Images
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin Tajani wanda ya wallafa a X a yau Asabar 2 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka
Italiya ta nuna damuwa kan yakin Iran
Ministan ya nuna damuwa kan ci gaba da yakin da ake yi yayin tattaunawarsa da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi.
Tajani ya ce bangarorin biyu sun tattauna kan rikicin Iran da sauran matsalolin yankin tare da bukatar hana rikicin kara kamari.
Tajani ya jaddada muhimmancin kara kaimi wajen tattaunawar diflomasiyya domin cimma yarjejeniya da kuma sake bude mashigin Hormuz cikin gaggawa domin tabbatar da zaman lafiya.
Ya yi gargadin cewa ci gaba da tangardar zirga-zirga a mashigar Hormuz na iya haddasa matsalar abinci da rashin kwanciyar hankali musamman ga kasashen Afrika masu tasowa.

Source: Getty Images
Goyon bayan da Italiya za ta ba Iran
Ministan ya bayyana cewa Italiya ba za ta amince da Iran ta bunkasa shirin nukiliya domin amfani da shi wajen aikin soja ba saboda hadarin gasar makaman nukiliya.
Tajani ya kuma bukaci Iran ta yi amfani da tasirinta kan kungiyar Hezbollah domin dakatar da hare-haren Isra’ila tare da samar da zaman lafiya ta hanyar sulhu a Lebanon.

Kara karanta wannan
Iran ta karyata Amurka kan asarar da Trump ya yi a yaƙin Isra'ila, ta fadi adadin dalolin
Tajani ya ce:
“Na bayyana karara cewa ga Italiya, ci gaban shirin nukiliyar Iran domin manufar soja wata jan layi ce, saboda akwai barazanar haddasa wata mummunar gasar makaman nukiliya a yankin.
“Italiya na ci gaba da kara himma wajen tallafa wa duk wani kokari na kasa da kasa domin samar da zaman lafiya, tare da ci gaba da bude hanyoyin tattaunawa da dukkan abokan hulda da kuma inganta zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.”
Ya kara da cewa Italiya za ta ci gaba da goyon bayan duk wani kokarin duniya na samar da zaman lafiya tare da bude hanyoyin tattaunawa da kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
Iran ta ƙaryata iƙirarin Amurka
Mun ba ku labarin cewa kasar Iran ta zargi Amurka da karya kan kudin da aka kashe yayin yakin Jamhuriyar Musulunci da Isra'ila.
Iran ta ƙaryata wasu rahotanni kan asarar da Donald Trump ya yi tana cewa gwamnatinsa ta boye hakikanin adadin kuɗin.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce yakin ya jefa iyalan Amurka cikin karin kashe kudade, yana cewa kowane gida na biyan dala 500.
Asali: Legit.ng