Ango ya saki amaryarsa a wurin walimar daurin aure

Ango ya saki amaryarsa a wurin walimar daurin aure

Wani aure da aka daura kuma ya mutu cikin mintuna uku kacal a kasar Kuwait, ya shiga cikin kundin tarihin duniya na auren da suka mutu cikin kankanin lokaci.

Wannan abin takaicin ya faru ne bayan angon ya fusata tare da yin amfani da kalmar zagi (stupid) a kan amaryarsa a wurin walimar daurin aurensu.

Ango da amaryar sun kasance ma'aurata da rayuwar aurensu ta fi kowacce rashin tasiri bayan aurensu ya mutu minti uku kacal da daura wa.

Kafafen yada labarai na kasar Kuwait sun ce amaryar ce ta nemi angon ya sake ta bayan ya yi amfani da lafazin zagi a kan ta saboda kawai ta yi tuntube, ta kusa fadu wa kasa a wurin walimar da suka shirya bayan sun saka hannu a kan takardar kulla yarjejeniyar aure.

DUBA WANNAN: Wata matar aure ta nemo wa mijinta mata ta biyu da zata kula da shi yayin da ta dauki juna biyu

Rahotannin sun bayyana cewa cikin hawaye, amaryar ta nemi angon ya sawwake mata, kuma nan take alkalin da ya jagoranci daura musu auren ya raba shi ba tare da wani bata lokaci ba.

Da jama'a ke bayyana ra'ayinsu a kan mutuwar auren a dandalin sada zumunta, sun bayyana cewa amaryar ta yi daidai da ba ta bata lokaci ta hanyar zama a cikin auren da babu mutunci da ganin girmanta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel