Fatuhu: Abin da ya sa na ajiye aiki na domin in yi takara a APC a Daura

Fatuhu: Abin da ya sa na ajiye aiki na domin in yi takara a APC a Daura

Fatuhu Mohammed, ‘Da ne a wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma mai wakiltar Mazabar Daura/Sandamu a majalisar wakilan tarayya ya yi wata hira da Daily Trust kwanan nan.

A wannan hira da ya yi, ‘dan majalisar ya bada labarin siyasarsa tare da magana a kan matsalolin rashin tsaro a Najeriya. ‘Dan majalisar ya dauki shugaba Buhari uba, ‘danuwa, kuma Maigidansa.

Honarabul Fatuhu Mohammed ya na alfaharin cewa shi kadai ne ‘dan majalisar da shugaba Buhari ya kadawa kuri’a a zaben 2019 domin shi ne ke wakiltar Mazabar ta sa ta jihar Katsina.

Mohammed ya na ganin cewa rashin tsaro ya na nema ya mamaye ko ina a Nahiyar Afrika da Duniya baki daya, inda ya ce wannan matsala ba ta ta’alakka da cikin Najeriya kadai ba.

A cewarsa, ya kamata Sarakuna da manyan Arewa su zauna su shawo kan wannan matsaloli na rashin tsaro kamar yadda a ka yi a zamanin baya. Mohammed ya ce akwai bukatar a nemi mafita.

KU KARANTA:Yadda Buhari zai kasa mukaman Ministoci a Gwamnatinsa

Da ‘Yan jarida su ka tambayi ‘dan majalisar ko ba ya ganin bukatar gwamnatoci su kara kokari sai ya nuna cewa majalisar da ta shude ta rika kawowa wannan gwamnatin ta APC matsala a 2015.

An yi wa sabon ‘dan majalisar tamabaya a game da abin da ya kai shi siyasa, sai ya bayyana cewa dole ya ajiye aikin gwamnatin da ya ke yi bayan da jama’a su ka taso shi a gaba ya nemi kujera.

Ya ce mutane sun yaba ne da kokarin da gidauniyarsa ta rika yi, don haka a ka tunzura sa ya tafi majalisar wakilan tarayya. Daga nan ne ya saye fam, har ya samu shugaba Buhari ya fada masa.

Kamar yadda ya fada, ko da ya fadawa shugaban kasar shirinsa na takara, sai ya ce da shi, bai da kudin da zai ba shi, sai dai ya taya sa da addu’a. Haka a ka yi, ya shiga takara ya yi nasara a 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel