Karamin ma'aikacin soja ya kashe direban mota a jihar Kogi

Karamin ma'aikacin soja ya kashe direban mota a jihar Kogi

Tsautsayi gami da bacin rana sun auku a jihar Kogi yayin da wani karamin ma'aikacin soja Kofura Moses, ya sokawa wani direban mota Ogbimi wuka a ciki wanda yayi sanadiyar mutuwar sa nan take bayan wata 'yar sa'insa ta shiga tsakani.

Tuni dai Kofura Moses ya ji matsa yayin da shiga hannun hukuma a garin Okene na birnin Lakwaja.

Takaddamar wannan lamari ta auku biyo bayan neman jin bahasin yadda wata mota mallakin marigayi Ogbime ta lalace a bisa hanya da ta yi sanadiyar kartar jikin motar karamin ma'aikacin na soji.

Nan da nan cacar baki ta barke a tsakanin su inda cikin fushi tare da hawa dokin zuciya Kofura Moses ya burmawa marigayi Ogbimi wuka a ciki kuma ya arce abunsa.

KARANTA KUMA: 'Dan uwan Sarki Salman na Saudiya ya rasu

Mashaida wannan tsautsayi ba su yi wata-wata ba wajen kurewa Kofura Moses gudu bayan ya arce cikin dokar daji kuma aka yi nasarar damke shi a bayan wani gini cikin yankin Agbede na jihar Edo.

A watan Agustan 2018 ne aka samu nasarar cafke wani soja daya tare da wasu mutane biyu dumu-dumu suna tsaka da aikata laifin fashi da makami na karkatar da wata tankar mai da tayi dakon litar man fetur 44,000 a jihar Legas.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel