Cin fuska ne Kasar Iran ta ce Najeriya ta mika mata Ibrahim Zakzaky

Cin fuska ne Kasar Iran ta ce Najeriya ta mika mata Ibrahim Zakzaky

Wata kungiya mai zaman kan-ta a Najeriya mai suna “The Campaign for Democracy” watau CD, ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Iran ta dauka, na kira a mika mata Sheik Ibrahim El-Zakzaky.

Kwanakin baya Iran ta nemi Najeriya ta ba ta babban Malamin nan na Shi’a watau Ibrahim El-Zakzaky. Wannan kungiya mai rajin kare damukaradiyya a Najeriya ta ce wannan magana ba ta dace ba.

Alhaji Abdullahi Jabi wanda ke shugabantar wannan kungiya ta “The Campaign for Democracy,” ya bayyana cewa maganar da kasar ta Iran ta yi, yana iya jawo sa-in-sa tsakanin manyan kasashen.

Abdullahi Jabi ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi hira da Manema labarai a Garin Minna da ke cikin jihar Neja a Ranar Lahadi, 28 ga Watan Yuli, 2019. Jabi ya ce ba da molon kai Najeriya ta ke aiki ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ba 'yan shi'a shawarar abin da ya kamata su yi

A hirar da Abdullahi Jabi ya yi da ‘yan jarida, ya nuna cewa Najeriya ta na amfani ne da dokar kan ta. Jabi ya ke cewa: “Najeriya ba gandun dabbobi bace, kasa ce mai aiki da dokoki masu zaman kan-su.”

Shugaban kungiyar ta CD ya cigaba da cewa: “Don haka kiran da Iran ta ke yi na a damka mata Ibrahim (El-Zakzaky), ya na iya jawo mata rikici da Najeriya. Ko da dai wannan kira sam bai ba mu mamaki ba.”

Ya ce: “Domin Kasar Iran ce Hedikwatar kungiyoyin Mabiya Shi’a a Duniya, inda El-Zakzaky da mutanensa su ka yi wa mubaya’a. Jabi ya kuma soki zanga-zangar da ‘yan shi’a ke yi, ya ce jawo rashin rayuka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel