Abin da Trump Ya Ce kan Sharuddan Iran Na Kawo Karshen Yaki da Amurka
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan kokarin kawo karshen yakin kasarsa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Donald Trump ya bayyana cewa Amurka na duba sababbin sharuddan da Iran ta gabatar domin kawo karshen yakin
- Sai dai, duk da haka Trump ya yi gargadin cewa Amurka za ta iya dawowa kai hare-hare kan Iran idan kasar ba ta yi abin da ya dace ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan kawo karshen yaki da Iran.
Trump ya bayyana cewa yana nazari kan sharudda 14 da Iran ta bayar domin kawo ƙarshen yaƙin da yake yi da ƙasar.

Source: Facebook
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a Florida kafin ya shiga jirgin Air Force One ranar Asabar, 2 ga watan Mayun 2026.
Me Trump ya ce kan tayin Iran?
Shugaba Trump ya tabbatar da cewa an ba shi bayani kan “tsarin yarjejeniyar”, yayin da ya yi gargaɗin cewa Washington za ta iya sake dawo da hare-hare ta sama idan Tehran ta “yi ba daidai ba”.
Duk da buɗe ƙofar diflomasiyyar, shugaban na Amurka ya yi amfani da kakkausan kalamai game da yuwuwar komawa fafatawa, wadda aka dakatar tun bayan sanar da tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu ranar 7 ga watan Afrilun 2026.
Lokacin da aka tambaye shi ko za a ci gaba da kai hare-hare sai Trump ya ce:
“Idan suka yi wani abu maras kyau, akwai yuwuwar hakan (hare-haren) ya faru."
Trump ya ƙara da cewa Amurka tana “samun nasara sosai” kuma ya yi iƙirarin cewa Iran tana matuƙar buƙatar sasanci saboda yaƙin da aka kwashe watanni ana yi da kuma killace hanyar teku ya “raunata” ƙasar.
Trump na son a hukunta Iran
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social daga baya, Trump ya ce yana da wuya a yi tunanin cewa shawarwarin na Iran za su kasance karɓaɓɓu, domin kuwa Tehran “ba ta biya babban farashi da ya dace ba kan abin da suka yi wa Bil-Adama da kuma Duniya a cikin shekaru 47 da suka gabata.”

Kara karanta wannan
Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka
Rahotanni sun bayyana cewa shirin mai dauke da abubuwa 14 na Tehran ya buƙaci a janye killace ta da Amurka ta yi ta hanyar teku, biyan diyyar yaƙi, da kuma sakin dukkan kadarorinsu da aka rike.
Haka kuma tana neman wa’adin kwanaki 30 don kammala sharuɗɗan zaman lafiyar, wa’adin da ya saɓa da zaɓin Washington na son a ɗauki lokaci mai tsawo ana tattake wuri.

Source: Getty Images
Ana fargabar yaki zai iya sake barkewa
Wannan ƙoƙari na diflomasiyya yana zuwa ne a daidai lokacin da ake cikin wata yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni ta mako uku wadda ta dakatar da yaƙin Amurka da Isra’ila a kan Iran, wanda aka fara a ƙarshen watan Fabrairun 2026.
Duk da tsagaita wutar, rundunar tsaron juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta bayyana ranar Asabar cewa tana nan cikin “shiri na ko-ta-kwana” don komawa fafatawa, tana mai nuni da rashin mutunta yarjejeniyoyin baya daga bangaren Amurka.
Iran ta karyata Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta karyata Amurka kan asarar da ta yi sakamakon yakin da ya barke tsakaninsu.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya zargi Amurka da boye hakikanin kudin yakin da ake yi tare da hadin gwiwa da Isra'ila.
Araghchi ya bayyana cewa ana yada labaran karya kan asarar Amurka yana cewa Pentagon na karya kan adadin dalolin da aka kashe.
Asali: Legit.ng
