Zaben 2027: Kwankwaso Ya Musanta Fitowa Takarar Shugaban Kasa a Inuwar ADC

Zaben 2027: Kwankwaso Ya Musanta Fitowa Takarar Shugaban Kasa a Inuwar ADC

  • Jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta jita-jitar ayyana takarar shugaban kasa
  • Kwankwaso ya tabbatar da cewa har yanzu bai yanke shawarar tsayawa takara ko yi wa wani mataimaki a jam'iyyar ADC ba
  • Madugu ya kuma yi karin haske kan rashin gab'ninsa a tarukan jam'iyyar ADC na baya-bayan nan, inda ya ce ya sanar da shugabanni

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria – Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa ba a halin yanazu.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na NNPP ya kuma tabbatar da cewa bai goyi bayan kowane dan takara ba, yana mai cewa duk wata jita-jita kan hakan “ba ta da tushe.”

Kwankwaso.
Madugun Kwankwasiyya, Snaata Rabiu Musa Kwankwaso yana magana a wurin taro Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

The Cable ta ce wannan na zuwa ne bayan rade-radin da suka yadu tun bayan taron jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, jihar Oyo, inda ake danganta shi da yiwuwar hadakar tikiti da tsohon dan takarar LP, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi karin haske kan jita jitar koma wa NDC da Obi domin yin takara

Jita-jitar ta kara karfi a kwanakin nan, inda magoya bayan ’yan siyasar biyu ke yada fastocin yakin neman zabe a kafafen sada zumunta.

Kwankwaso ayyana neman takara a ADC?

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a daren jiya Asabar, 2 ga watan Mayu, 2027, Kwankwaso ya yi watsi da rahotannin, yana mai cewa babu wata matsaya ta karshe da aka dauka kan makomarsa ta siyasa.

Kwankwaso ya kara da cewa sabanin abin da ake yadawa, jam’iyyar ADC ba ta yanke shawara kan tikitin shugaban kasa ba ko kumata zabi dan takara ba.

“Ban bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa ba, kuma ban goyi bayan kowa ba. Duk wata jita-jita kan hakan ba ta da tushe.”

Ya kuma yi tsokaci kan hukuncin kotun koli da ya mayar da rikicin shugabancin ADC zuwa babbar kotun tarayya, yana mai cewa hakan ya jefa jam’iyyar cikin mawuyacin hali.

Madugun Kwankwasiyya.
Tsohon 'dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a taron Kwankwasiyya a Kano Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Dalilin rashin halartar tarukan ADC

Dangane da rashin halartar wasu tarukan jam'iyyar ADC, Kwankwaso ya ce hakan ya faru ne saboda wasu uzurori na kashin kansa kuma ya riga da ya sanar da shugabannin jam’iyyar tun farko.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Kwankwaso ya gama yanke shawara, zai bar ADC tare da Peter Obi

Ya jaddada cewa duk wani hukunci da zai dauka kan tafiyarsa ta siyasa za a sanar da shi ne ta hanyoyin da suka dace, ba wai ta jita-jita ba.

Kwankwaso na shirin komawa jam'iyyar NDC?

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani kan wasu rahotanni da ke cewa zai koma NDC.

Sai dai Kwankwaso ya ce babu wata matsaya ta ƙarshe da aka cimma kan makomarsa ta siyasa ko ta magoya bayansa zuwa yanzu.

Jagoran yan Kwankwasiyyya ya bayyana cewa matsalar shari'o'i da rikicin gida da ya sa suka bar jam'iyyar NNPP, yanzu ita ADC ta fama da wadannan rigingimu, inda ya ce sun fara laluben mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262