'Dan uwan Sarki Salman na Saudiya ya rasu

'Dan uwan Sarki Salman na Saudiya ya rasu

Kasar Saudiya a ranar Litinin ta dugunzuma cikin shirye-shiryen gudanar da jana'izar 'dan uwa na jini da ya kasance babban Yaya ga Sarki Salman, wanda ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 96.

Mai Martaba Yarima Bandar bin Abdulaziz al-Saud, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Lahadi kamar yadda masarautar kasar ta bayyana cikin wata 'yar takaitacciyar sanarwa da kafar watsa labarai ta Saudi Press ta gabatar.

Za a gudanar da sallar jana'izar sa a ranar Litinin 29 ga watan Yuli cikin babban masallaci mai alfarma da ke garin Makkah.

Marigayi Yarima Bandar yayin rayuwarsa ya kasance babban 'da ga masarautar Saudiya ta Sarki Abdulaziz.

Masarautar kasar ba ta fayyace sillar rasuwar sa ba, sai dai kafofin watsa labarai na kasar sun bayyana cewa marigayi Bandar ya cika bayan wata tsawaitacciyar rashin lafiya da ya dade yana fama da ita.

KARANTA KUMA: Hatsari a Maigatari: Rayuka 7 sun salwata, Mutane 11 sun jikkata a Jigawa

Manya 'ya'yansa biyu na rike da manyan mukamai a gwamnatin kasar inda Yarima Faisal bin Bandar ya kasance gwamnan Riyadh yayin da kuma Yarima Abdullah bin Bandar ya kasance shugaban cibiyar tsaro ta kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel