Shugaban hukumar INEC, Farfesa Yakubu zai samu lambar girma

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Yakubu zai samu lambar girma

-Shugaban hukumar zabe ta INEC da wasu mutum biyu za su karbi lambobin girma

-Za a karrama mutanen uku ne wurin babban taron NIPR a jihar Kaduna wanda aka saba yi a ko wace shekara

-Malam Zubairu Jibril, Sarkin Birnin Gwari shi ne zai kasance shugaban taron yayin da Gwamna El-Rufai za kasance babban bako na musamman

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu zai karbi lambar girma daga hannun Nigerian Institute of Public Relations (NIPR) a Kaduna, wurin taron da ta saba gabatarwa na shekara-shekara.

Har ila yau, akwai wasu mutum biyu da zasu samu wannan lambar girma, Injiniya Mansur Ahmad da kuma Injiniya Suleiman Husseni Adamu wanda sunansa ke cikin sabbin ministocin da Shugaban kasa ya zaba.

KU KARANTA:Rashin tsaro yana kawo koma bayan tattalin arziki – Gwamna Abiodun

Shugaban NIPR reshen jihar Kaduna, Bashir Chedi shi ne ya bada wannan sanarwa inda ya ce, za’a gudanar da taron a ranar Asabar 3 ga watan Agustan 2019. Taron dai za a yi shi ne babban dakin taron na gidauniyar Ahmadu Bello Sardauna dake garin Kaduna, yayin da Mallam Zubairu Jibril Mai-Gwari na II ( Sarkin Birnin Gwari) zai kasance shugaban taro.

Ya kara da cewa, za a bada lambobin girma ga mutane ukun ne kasancewar sun nuna jajircewarsu a wurin yiwa kasarsu aiki tukuru.

Shugaban ya cigaba da cewa, abinda za’a tattauna kansa a ranar shi ne: “ Farfado da kamfanonin Arewa, alal misali masaka,” wanda kuma zai yi magana a kan wannan batun shi ne gogaggen dan kasuwan jihar Kano, Alhaji Saidu Dattijo Adhama.

Kamar yadda Chedi ya fadi a cikin zancensa, an shirya wannan taron ne domin zaburar da arewacin Najeriya kan sake farfado da masakun da akwai a da amma yanzu duk sun mace.

Haka zalika, ana sa ran halartar Gwamna Nasiru El-Rufai a matsayin babban bako na musamman, inda kuma sauran gwamnonin jihohin arewa ake tsammanin kasancewarsu a wannan wuri.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel