Jerin sunayen ministoci: Tsohon hadimin Jonathan ya yaba wa Buhari

Jerin sunayen ministoci: Tsohon hadimin Jonathan ya yaba wa Buhari

- Tsohon hadimin Jonathan ya yi martani akan jerin sunayen zababbun inistocin shugaba Buhari

- Buhari a ranar Litinin, 22 ga watan Yuli, ya gabatar da jerin sunayen zababbun ministoci a gaban majalisar dattawa domin tabbatar da su

- Sai dai kuma Okupe ya bayyan cewa duk wanda ke sn zama minister, toh ya fara koyon yadda ake buga siyasa

Doyin Okupe, tsohon babban mai ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara akan harkokin waje, ya yi martani ga jerin sunayen zababbun ministoci 43 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura majalisar dattawa a ranar Litinin, 22 ga watan Yuli.

Legit.ng ta rahoto cewa yace akwai mata da maza da dama da suka nuna cancan da kuma karewa a cikin jerin sunyen koda dai ya bayyana cewa akwai yan tsirarun suneye da ke da ayar tambaya.

Okupe, wanda ya yi wa tsoon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar aiki a zaben kasar da ya gabata ya bayyana cewa,babu ko mutum daya cikin sunaye da aka ambata da aikata laifi a kowani kotun Najeriya.

Okupe yace siyasa ba sabon abu bane inda mutane ke buga tasu domin fin na saura, inda ya kara da cewa ba gasar nakasassu bane.

Tsohon hadimin tsohon Shugaban kasar ya kuma kara da cewar duk wanda ke son zama minista toh su bar jin dadinsu sannan su shiga tseren siyasa.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikatu 3 sun yi wa Fashola yawa, gashi yanzu kansu duk furfura ne - Okorocha

Ya kuma kara da cewa gwamnatin tarayya ta sanya sunayen ayyukan kowanne a jeri sunayen ministocin, inda ya kara da cewa da Shugaban kasar ya sani ya saki sunayen akalla makonni biyu zuwa uku kafin tura su majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatarwa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel