An Cafke Mai Taimakon 'Yan Bindiga a Katsina, an Same Shi da Kayan Tsafi

An Cafke Mai Taimakon 'Yan Bindiga a Katsina, an Same Shi da Kayan Tsafi

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wani mutum da ake zargi yana ba ‘yan bindiga bayanai wajen garkuwa da jama'a a jihar Katsina
  • Kakakin rundunar 'yan sanda, DSP Abubakar Sadiq-Aliyu ya yi karin bayani game da dabarun da suka yi wajen kama wanda ake zargin
  • DSP Abubakar Sadiq-Aliyu ya bayyana cewa wanda ake zargin, Abdullahi Abdullahi ya amince da aikata laifin tare da fito da wasu bayanai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sanda a Jihar Katsina ta kama wani mutum mai shekaru 28 da ake zargi da bayar da bayanai ga ‘yan bindiga, tare da kwato wasu kayan tsafi da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifi.

Hakan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro ke cigaba da farautar 'yan ta'adda a jihar Katsina da wasu sauran jihohin Arewa ta Yamma da ke fama da matsalar 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

2027: Shettima ya yi gargadi kan rusa APC bayan zaben fitar da gwani

Taswirar jihar Katsina
Taswirar jihar Katsina a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Punch ta wallafa cewa mai magana da yawun rundunar, DSP Abubakar Sadiq-Aliyu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina.

Wanda ke taimakon 'yan bindiga

DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce an kama wanda ake zargin, mai suna Abdullahi Abdullahi, ne bayan samun sahihan bayanai daga Hedikwatar ‘yan sanda ta Musawa.

Kakakin 'yan sanda ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa yayin bincike, inda ya ce yana hada kai da dan uwansa wajen aikata laifuffuka, ciki har da yi wa mutane barazana.

“Mun kira wani mutum muka nemi ya biya Naira miliyan 10, idan ba haka ba za mu kashe shi,”

In ji wanda ake zargin

Mai magana da yawun ya kara da cewa wanda ake zargin ya kuma amsa cewa yana da hannu a irin wadannan laifuffuka a baya.

Sufeton 'yan sandan Najeriya, Tunji Disu
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Tunji Disu a ofis. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Bayanin kwamishinan 'yan sanda

Kwamishinan ‘yan sanda, Umar Ali-Fage, ya ba da umarnin a kara kaimi wajen nemo da kama sauran wadanda suka tsere da ke da alaka da lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni da 'yan APC sun fitar da dan takarar gwamnan Yobe a 2027

Ali Fage ya sake jaddada kudirin rundunar na yaki da ‘yan bindiga, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu yana taimaka wa masu aikata laifi za a hukunta shi ba tare da sassauci ba.

Daily Post ta wallafa cewa kwamishinan ya bukaci al’umma da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani motsin miyagu ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Jihar Katsina da ke Arewa ta Yamma ta yi fama da matsalolin 'yan bindiga tsawon shekaru duk da shirin sulhu da aka yi da wasunsu.

Fulani 150 sun mutu a Kwara

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar Amnesty International da ke kare hakkin dan Adam ta yi zargin cewa Fulani 150 sun mutu a wani sansani a jihar Kwara.

Ta bayyana cewa an tara Fulanin ne a wani sansanin NYSC domin su samu mafaka bayan yawaitar hare-haren 'yan bindiga a yakunan da suke zaune.

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa sansanin ba a karkashin jami'anta ya ke ba, inda gwamnatin Kwara ta ce za ta yi bincike kan zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng