Latest
Mun samu labari cewa a jiya aka yi ram da wanda ya lalata kananan yara fiye da 30 a Neja. Jami’an ‘yan sanda na jihar Neja sun damke wannan Mutumi ne da laifin saduwa da Alamjirai a wata Makaranta.
A yayin da kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya matsa lamba wajen dinke barakar da ya samu a bara, kungiyarsa ta fanshi dan wasan bayan a kan fan miliyan 80.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta ta amince da rokon hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) na daskarar da asusun bankin First City Monument Bank (FCMB) mai lamba 0998552074 na gwamnati
Lauya mai kara, Emmanuel Ochayi ya bayyana ma kotun cewa Mando ya aikata haka ne a ranar 14 ga watan Yuli a daidai shataletalen Apo dake Abuja, inda daga bisani dansanda ASP Ashim Oliver ya kai karar direban.
Fitaccen jarumin fina finan Kannywood, Tanimu Akawu wanda a baya sunansa ya yi ta yawo a kafafen sadarwar zamani inda aka ruwaito cewa wai ya zargi matan Fim da bin maza masu kudi domin samun kudi, ya musanta wannan zargi.
Shugaban masu rinjayi a majalisar dokokin jihar Sokoto, Alhaji Bello Isa Ambarura yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi mutane masu mutunci na hakika a matsayin mambobin sabuwar majalisarsa.
Rundunar Yansandan Najeriya ta saki jerin lambobin wayoyin jami’an hulda da jama’a na rundunar dake dukkanin jahohin Najeriya 36 tare da babban birnin tarayya Abuja domin kai rahoto kai tsaye ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana abin da ya ware domin aikin RUGA. Ita Enang ya ce Gwamnatin nan ta kasafta Biliyan 2.2 domin aikin RUGA a fadin Najeriya a wannan shekara ta 2019.
Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun kai wani samame gidan tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari, dake garin Talatar Mafara domin gudanar da bincike.
Masu zafi
Samu kari