Gwamnatin Tarayya ta kasafta Biliyan 2.2 domin aikin RUGA a Najeriya – Enang

Gwamnatin Tarayya ta kasafta Biliyan 2.2 domin aikin RUGA a Najeriya – Enang

Ita Enang, wanda shi ne Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan harkokin majalisar dattawa a Najeriya, ya bayyana abin da a ka warewa shirin RUGA a kasafin kudin kasar na bana.

Sanata Ita Enang ya ke cewa Naira Biliyan 2.2 a ka kebe a cikin kasafin kudin Najeriya na 2019 saboda a gina RUGA da Makiyaya za su rika kiwon dabbobinsu. Yanzu dai an dakatar da wannan shiri.

Enang ya yi wannan kawabi ne a lokacin da ya gana da wasu ‘Daliban shari’a daga jiharsa ta Akwa Ibom a Abuja. Mai ba shugaban kasar shawara ya ce shirin RUGA ba na Fulani ko Hausa bane kurum.

Babban Mai taimakawa shugaban kasar ya kuma nunawa jama’a cewa an kirkiro kalmar RUGA ne tun a shekarar 1956 lokacin Turawa daga Ingilishi watau “rural grazing area” ma’ana wurin kiwo a karkara.

KU KARANTA: Abin da Obasanjo da Jagororin Fulanin Najeriya su ka tattauna a Abeokuta

Wannan na nufin babu wani shiri da gwamnatin Buhari ta ke da shi na Hausantar ko Musuluntar da Najeriya inji Ita Enang. Hadimin shugaban kasar ya ce don haka a ka ware Biliyan 2.258 a bana domin kiwo.

Tsohon Sanatan ya kuma nuna cewa ‘yan majalisa ba su adawa da wannan shiri da ya ke aiki tun 1979 domin kuwa sun sa da zamanshi, kuma sun amince da Biliyoyin kudin da a ka ware masa a wannan shekara.

Bayan wannan biliyan 2.2, gwamnatin Buhari ta kuma ware miliyan 300 domin tsabtace ruwan sha da kuma miliyan 400 na noman dankali da wasu miliyan 350 na noman citta a shekarar nan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel