Harry Maguire da 'yan wasan baya 4 mafi tsada a duniya

Harry Maguire da 'yan wasan baya 4 mafi tsada a duniya

Dan wasan kwallon kafa da kungiyar Manchester United ta kammala cefanensa a ranar Litinin, Harry Maguire, ya fi kowane dan wasan baya tsada a tarihin tamaula.

Kungiyar Manchester United ta sayo dan wasan na kasar Ingila daga kungiyar Leicester City a a kan zunzurutun kudi na Fan miliyan 80 daidai da dalar Amurka miliyan 97.

Ga dai jerin 'yan wasan baya biyar tsada a tarihi.

1. Harry Maguire

A yayin da kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya matsa lamba wajen dinke barakar da ya samu a bara, kungiyarsa ta fanshi dan wasan bayan a kan fan miliyan 80. Ta fanso Harry Maguire daga kungiyar kwallon kafa ta Leicester City a watan Agustan 2019.

2. Virgil van Dijk

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, ta fanso Virgil van Dijk, dan asalin kasar Netherland, daga kungiyar Southampton a kan dukumar dukiya ta fan miliyan 75 a a watan Janairun 2018. Dan wasan bayan ya taka rawar gani wajen taimakawa kungiyarsa lashe kofin zakarun Turai a bara.

3. Lucas Hernandez

Lucas Hernandez dan asalin kasar Faransa, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich daga kungiyar Atletico Madrid ta kasar Spain a kan kudi fan miliyan 68 a watan Yulin 2019. Lucas wanda yake da tagullar lashe gasar kofin duniya, ya bugawa kungiyar Atletico Madrid fiye da wasanni 100 kafin komawarsa kungiyar Bayern Munich mai buga gasar Bundesliga a Jamus.

4. Matthijs De Ligt

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus mai taka leda a kasar Italiya, ta yi cefanen Matthijs De Ligt daga kungiyar kwallon kafa ta Ajax a kan fan miliyan 67.5. Duba da yadda kasuwar 'yan kwallon kafa ke hawa da sauka daidai da tsare-tsare irin nata, akwai yiwuwar farashin dan wasan na kasar Netherlands zai haura zuwa fan miliyan 77.

5. Aymeric Laporte

A watan Janairun 2018 ne Aymeric Laporte ya baro kungiyar kwallon kafa ta Athletic Bilbao dake kasar Spain inda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dake kasar Ingila a kan kudi fan miliyan 57. Tun bayan zuwansa kasar Ingila, Laporte ya samu lambar yabo yayin da kungiyar Manchestrer City ta lashe gasar kofukan Premier League, Charity Cup da kuma FA Cup.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel