Yansanda sun damke wani direban bankaura daya kashe mutane 3 a Abuja

Yansanda sun damke wani direban bankaura daya kashe mutane 3 a Abuja

Rundunar Yansandan Najeriya ta kama wani mutumi dan shekara 37 mai suna Celestine Mando tare da gurfanar dashi gaban kotun majitsri dake unguwar Wuse Zone 6 a kan tuhumar da take yi masa na kashe mutane 3 a sanadiyyar tukin ganganci.

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito Celestine Mando mazaunin garin Abuja ne, kuma yana zaune ne a gida mai lamba 92 a rukunin gidajen NPI dake unguwar Gaduwa.

KU KARANTA: Tanimu Akawu ya musanta zargin Hadiza Gabon da Maryma Yahaya da karuwanci

Lauya mai kara, Emmanuel Ochayi ya bayyana ma kotun cewa Mando ya aikata haka ne a ranar 14 ga watan Yuli a daidai shataletalen Apo dake Abuja, inda daga bisani dansanda ASP Ashim Oliver ya kai karar direban.

Lauya Ochayi yace: “Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake gudanar da bincike ababen hawa a kan shataletalen, inda Mando ya tuko motarsa a guje, motar da bata ko lamba, kuma ya buga ma wata mota kirar Golf II dake da lamba KDG 152 XA.

“Nan da nan motar Golf II ta kama da wata, inda direban motar, Mohammed Fanari da fasinjoji 2 dake cikin motar suka mutu bayan sun kone, konewa kurmus. Laifin ya saba ma sashi na 27 da 29 na dokokin tuki a Najeriya.” Inji shi.

Daga karshe Alkalin Kotun Omolola Akindele ya bada belin direban a kan N500,000 da kuma mutane biyu da zasu tsaya masa, daya ya kasance ma’aikacin gwamnati dake mataki na GL14 yayin da na biyun kuma ya kasance dan kasuwa mai kadara a yankin AMAC, sa’annan ya dage karar zuwa 20 ga watan Agusta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel