Ba Sassauci: Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Bama Bamai kan 'Yan ISWAP, an Kashe Tantirai Masu Yawa

Ba Sassauci: Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Bama Bamai kan 'Yan ISWAP, an Kashe Tantirai Masu Yawa

  • Dakarun sojojin sama na Najeriya sun kai wasu hare-hare masu zafi kan 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno da ke yankin Gabas
  • Sojojin saman sun samu nasarar rage mugun iri ta hanyar kashe wasu daga cikin 'yan ta'addan bayan sun yi musu ruwan bama-bamai daga sama
  • Dakarun sojojin saman sun samu gagarumar nasara bayan da suka jefo bama-bamai kan 'yan ta'addan, lamarin da ya jawo aka kashe da dama daga cikinsu

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno, Najeriya - Dakarun sojojin sama na Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun kashe sama da ‘yan ta’addan ISWAP 30 a jerin wasu hare-hare da aka kai a yankin Tafkin Chad na jihar Borno.

Sojojin sama sun kashe 'yan ta'addan ISWAP a Borno
Jiragen rundunar sojojin saman Najeriya Hoto: Sodiq Sulaimon
Source: Getty Images

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a wani rubutu a shafinsa na X a ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun toshe kofofin tsira ga 'yan ta'adda yayin da aka hallaka tsageru masu yawa

Sojoji sun farmaki 'yan ta'addan ISWAP

Farmakin sojojin ya biyo bayan “sahihan bayanan sirri, sa ido da kuma bincike” da suka nuna ƙaruwar ayyukan ta’addanci, gami da jigilar kayan aiki ta hanyoyin ruwa a kewayen yankin tsibirin Kaniram.

An tura abubuwan sanya ido zuwa yankin baki ɗaya inda suka tabbatar da ganin kusan jiragen ruwa 31 da aka ajiyesu a gefen ruwa, tare da zirga-zirgar mutane da suka yi daidai da mayakan ISWAP.

Bayan tantancewa, sashen ayyukan sama ya ƙaddamar da hare-haren kwarewa daidai da ƙa'idojin yaƙi da aka kafa da kuma hanyoyin kai hari, jaridar TheCable ta dauko labarin.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan ISWAP

Harin farko ya yi nasarar tarwatsa matattarar ‘yan ta’addan tare da raunana ƙarfin jigilar kayayyakin su ta hanyar lalata jiragen ruwa da dama da ake amfani da su wajen zirga-zirga da samar da kayayyaki ta hanyoyin ruwa.

Ƙarin sa ido na ISR ya nuna yunƙurin da ‘yan ta’addan suka yi na sake haɗuwa a cikin wasu bishiyoyi na kusa. Sakamakon haka, an gudanar da wasu hare-haren biyo baya.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da 'yan bindiga suka kai sababbin hare-hare a Plateau aka rasa rayuka

Sojojin sama sun kashe 'yan ta'addan ISWAP
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hari na biyu ya farmaki wasu ‘yan ta’adda kusan takwas inda aka kashe su, yayin da aka ga wasu suna guduwa zuwa wuraren ɓuya.

Harin na uku kuma ya afka wa wani rukunin ‘yan ta’adda kusan 15 da suka fake a ƙarƙashin bishiyoyi, inda aka kashe su.

Sojoji sun kama mataimakin jagoran 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke mataimakin wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Kachalla Auta, tare da matarsa a jihar Gombe.

Dakarun sojojin sun kama mutanen ne biyo bayan wani samame na musamman da aka gudanar ta hanyar amfani da bayanan sirri a wurare daban-daban.

Majiyoyi sun bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin, da aka bayyana sunayensu a matsayin Bala, wanda aka fi sani da “Pakapaka,” da kuma matarsa Zulaiha Bala, bayan da suka tsere daga dajin Madami da ke jihar Plateau.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng