'Ba Korarsu Aka Yi ba," Gwamnati Ta Faɗi dalilin Murabus ɗin Dangiwa da Wale Edun

'Ba Korarsu Aka Yi ba," Gwamnati Ta Faɗi dalilin Murabus ɗin Dangiwa da Wale Edun

  • Fadar Shugaban Ƙasa ta warware rudanin da aka samu game da 'murabus' din Ministan kuɗi, Wale Edun, da takwaransa na gidaje, Ahmed Dangiwa
  • A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, ba Shugaba Bola Tinubu ne ya kori Edun da Dangiwa ba
  • Sanarwar dai ta bayyana cewa Wale Edun da kansa ya miƙa wa Tinubu takardar murabus a ranar Litinin, lokacin da ya cika shekaru 70 a duniya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Fadar Shugaban Ƙasa ta fito da warware rudanin da aka samu game da sauye-sauyen da aka samu a majalisar zartarwa ta tarayya.

Aso Rock Villa ta bayyana cewa Mista Wale Edun da Ahmed Dangiwa, sun yi murabus ne daga muƙamansu, kuma a ƙashin kansu.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: ICIR ta fallasa 'boyayyun dalilan' Tinubu na tsige ministoci 2

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Wale Edun da Ahmed Dangiwa su suka yi murabus ba korarsu aka yi ba.
Ahmed Dangiwa, tsohon ministan gidaje (hagu), Shugaba Bola Tinubu (tsakiya) da Wale Edun, tsohon ministan kudi (dama). Hoto: @Arch_Dangiwa/X, Getty Images, @FinMinNigeria/X
Source: UGC

Wannan sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar a shafinsa na X, ta zo ne domin musanta rahotannin da ke cewa korarsu aka yi.

Dalilin murabus din Wale Edun

Tsohon Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya miƙa takardar barin aikinsa ne a ranar Litinin, wadda ta yi daidai da ranar da ya cika shekaru 70 a duniya, a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ce:

"Edun ya bayyana cewa matsalolin lafiya da yake fuskanta ne suka tilasta masa ajiye aikin domin ya samu damar kula da kansa da kuma mayar da hankali kan harkokinsa na kashin kai.
"Kafin ya tafi, Edun ya gana da Shugaba Tinubu na tsawon sa'a guda a fadar Aso Rock Villa, inda ya gode wa shugaban bisa damar da ya ba shi na taimaka wa Najeriya ta zama mai ƙarfi da daraja a idon duniya.
"Edun, wanda gogajen ma'aikacin banki ne, ya taɓa zama kwamishina a ƙarƙashin Tinubu a Legas, kuma ya yi aiki a Babban Bankin Duniya."

Kara karanta wannan

Ahmed Dangiwa ya yi martani da Tinubu ya tsige shi daga mukamin minista

Dalilin murabus din Ahmed Musa Dangiwa

Sanarwar ta kuma ce shi ma tsohon ministan gidaje da raya birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya miƙa tasa takardar murabus ɗin tare da godiya ga shugaban ƙasa.

Fadar shugaban kasa ta ce ba Tinubu ne ya kori Ahmed Dangiwa da Wale Edun daga ministoci ba.
Shugaba Bola Tinubu ya na jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Dangiwa, wanda ƙwararren injiniyan gine-gine ne, ya taɓa zama shugaban Bankin Gidaje na Tarayya (FMBN) da kuma sakataren gwamnatin jihar Katsina kafin naɗinsa a matsayin minista a watan Agustan 2023.

Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin nasu tare da yi musu fatan alheri, inda ya bayyana jin daɗinsa kan yadda suka jajirce wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙi na gwamnatinsa.

Karanta sanarwar Onanuga a nan kasa:

Tinubu ya nada sababbin ministoci

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya ta sanar da sunayen sababbin ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada domin maye gurbin Wale Edun da Ahmed Dangiwa.

Tinubu ya amince da nadin Taiwo Oyedele, wanda kafin yanzu shi ne Karamin Ministan Kudi, domin ya zama Ministan Kudi kuma babban minista mai kula da tattalin arzikin kasa.

Haka zalika, Tinubu ya nada Muttaqa Rabe Darma (PhD) a matsayin wanda zai shugabanci Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com