Bayan 'Sallamar' Mutum 2, An Kara Samun Ministan da Ya Yi Murabus a Gwamnatin Tinubu

Bayan 'Sallamar' Mutum 2, An Kara Samun Ministan da Ya Yi Murabus a Gwamnatin Tinubu

  • Adebayo Adelabu ya yi murabus daga mukaminsa na ministan harkokin makamashi domin neman takarar gwamna a jihar Oyo
  • Adelabu ya mika takardar ajiye aikinsa a hukumance ga sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, yau Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026
  • Ya ba da shawarar kirkiro mukamin Ministan Makamashi mai kula da dukkan fannoni domin hada kai wajen gyaran bangaren wuta, gas da sauran fannoni

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin mayar da hankali kan takarar gwamna a jihar Oyo

Hakan na kunshe ne a cikin wasikar murabus dinsa mai dauke da ranar 22 ga Afrilu, 2026, wacce ya mika wa Shugaba Bola Ahmed Tinububa hukumance.

Ministan wutar lantarki.
Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu yana ganawa da wasu masu ruwa da tsaki a ofishinsa a Abuja Hoto: Adebayo Adelabu
Source: Twitter

Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa a cikin wasikar, Adelabu ya bayyana cewa murabus din nasa zai fara aiki daga ranar 30 ga Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan

Kurunkus: An gurfanar da mutane 6 da ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

Dalilin Adelabu na ajiye kujerar minista

Rahotanni sun nuna cewa ministan ya sanar da shirinsa na yin murabus bayan ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ya gabatar da rahoton ayyukansa na shekaru biyu da rabi a bangaren wutar lantarki.

A wasikar da ya mika wa Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume, Adelabu ya ce matakin ya dace da dokar zabe ta 2026 da ta hana masu rike da mukaman gwamnati tsayawa takara.

Ya kuma bayyana cewa burinsa na zama gwamna ya samo asali tun shekarar 2016 lokacin da yake mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

Tsohon ministan ya ba Tinubu shawara

Ministan ya ba da shawarar kirkiro mukamin Ministan Makamashi mai kula da dukkan fannoni domin hada kai wajen gyaran bangaren wuta, gas da sauran fannoni masu alaka.

Ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da daidaito a manufofi da aiwatar da tsare-tsare masu amfani da ka iya warware matsalar makamashi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku da Kwankwaso na tsaka mai wuya, Kotun Koli ta zo matakin karshe kan rikicin ADC

Wasu nasarorin da Adelabu ya samu

Adelabu ya lissafa nasarorin da aka samu a lokacin mulkinsa, ciki har da aiwatar da dokar wutar lantarki ta 2023 wadda ta bai wa jihohi damar shiga harkar samar da wuta.

Ya ce samar da wuta ya karu zuwa sama da megawatt 6,000, tare da inganta hanyoyin rarraba da watsa wutar lantarki, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Adelabu.
Minista a Najeriya, Adebayo Adelabu lokacin da ya mika takardar murabus ga sakataren gwamnatin tarayya, Geroge Akume a Aso Rock Hoto: @AdeeOneAdekooto
Source: Twitter

Haka kuma, ya ce an samu karuwar kudaden shiga daga Naira tiriliyan 1 a 2023 zuwa Naira tiriliyan 2.3 a 2025 sakamakon gyaran tsarin farashin wuta da sake fasalin basussuka.

A karshe, Adelabu ya gode wa shugaban kasa bisa damar da aka ba shi na yi wa kasa hidima, yana mai cewa lokaci ne da ya ba shi damar bayar da gudunmawa wajen ci gaban Najeriya.

Da gaske Tinubu ya kori ministoci 2?

A wani labarin, kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta warware rudanin da aka samu game da 'murabus' din Ministan kuɗi, Wale Edun, da takwaransa na gidaje, Ahmed Dangiwa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An 'gano' dalilin Tinubu na sallamar ministan kudi a Najeriya

Sabanin yadda ake yadawa cewa Tinubu ya kore su daga aiki, ta bayyana cewa Mista Wale Edun da Dangiwa, sun yi murabus ne daga muƙamansu bisa ra'ayin kansu.

Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin nasu tare da yi musu fatan alheri, inda ya bayyana jin daɗinsa kan yadda suka jajirce wajen aiwatar da sauye-sauyen gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262