Abin da ya sa na daina kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Dan takarar PDM

Abin da ya sa na daina kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Dan takarar PDM

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDM a yayin babban zaben kasa na 2019, Fasto Aminchi Habu, ya bayyana dalilin da ya sanya ya janye korafin rashin amincewa da sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a watan Fabrairu.

Fasto Aminchi ya bayyana yarjejeniyar da suka kulla tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari wadda ta sanya ya janye korafin da ya gabatar a gaban kotu na rashin amincewa da sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

A baya dan takarar tare da jam'iyyar sa ta PDM sun shigar da korafi a gaban kotun daukaka karar zabe da ke zamanta a garin Abuja. Masu korafin sun nemi kotu ta yi watsi da nasarar shugaban kasa Buhari biyo bayan kuskuren da aka tafka na rashin sanya hatimin jam'iyyar a takardun kada kuri'a.

Cikin wani korafi mai lamba CA/PEPC/004/2019, jam'iyyar PDM ta nemi kotun daukaka karar zabe da a sake gudanar da wani sabon zabe a kasar a sakamakon rashin sanya hatiminta a takardun kada kuri'a da hakan ya yi tasiri wajen haramta mata takara bayan makudan kudin da ta narkar wajen gudanar da yakin neman zabe.

Sai dai a yayin da kotun daukaka karar zaben ke shirin fara sauraron karar a ranar 24 ga watan Yuli bisa jagorancin Mai Shari'a Muhammad Garba, jam'iyyar PDM ta bayar da sanarwar janye korafin da ta gabatar na kalubalantar nasarar shugaba Buhari.

Ba tare da bayyana wani dalili ba, masu korafin sun shaidawa kotun cewa samuwar wata hanya da za ta share masu hawaye ya sanya suka janye korafinsu daga gabanta.

Hakazalika babu ko daya daga cikin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, shugaban kasa Buhari ballantana kuma jam'iyyarsa ta APC da suka nemi bahasin yadda wannan lamari ya kasance.

KARANTA KUMA: Sauke nauyin da rataya a wuyanmu ya sanya muka kai simame gidan tsohon gwamna Yari - EFCC

Sai dai a yayin wata hira da manema labarai a cikin garin Abuja, Fasto Aminchi ya ce alkawalin da shugaba Buhari ya yi masa na inganta tsaro a yankin Arewacin Najeriya da mafi akasarin al'ummar yankin suka kasance mabiya addinin Kirista kamar Kudancin Kaduna, ya sanya ya janye korafin sa babu wata-wata.

Bugu da kari ya ce shugaba Buhari ya sha alwashin bayar da mafificin muhimmanci wajen habaka ingancin zamantakewa da kuma gine-gine a yankunan. Ya musanta zargin cewa kudi fadar shugaban kasa ta shaka masa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel