Yara fiye da miliyan daya basa zuwa makaranta a Kano - UNICEF

Yara fiye da miliyan daya basa zuwa makaranta a Kano - UNICEF

Wakilin ofishin majalisar dinkin mai kula da kashe kudi domin inganta rayuwar kananan yara (UNICEF) a jihar Kano, Peter Hawkins, ya bayyana cewa akwai yara fiye da miliyan daya da basa zuwa makaranta a jihar Kano.

Mista Hawkins ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata bita ta kwanaki hudu da kwamishinoni da manyan sakatarorin gwamnati daga jihohin arewa 19 ke halarta a jihar Kano.

Ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tarayya ce ta shirya taron tare da hadin gwuiwar gwamnatin jihar Kano da hukumar UNICEF.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa an shirya taron ne domin tabbatar da samun tsari mai dorewa da zai inganta rayuwar kananan yara a arewacin Najeriya.

Mista Hawkins ya ce UNICEF ta samu alkaluman adadin yaran da basa zuwa makarantar boko yaki da jahilci ne daga ma'aikatar ilimi ta kasa.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun tarwatsa wadanda suka fito zanga-zangar juyin hali (Hotuna)

Ya bayyana cewa akwai bukatar Najeriya ta rubanya kokarinta a bangaren magance matsalar yawan yaran da basa zuwa makaranta ta hayanyar kara saka jari a bangaren ilimi.

"Saka hannun jari a bangaren ilimi tamkar saka hannun jari ne a gyara goben kasa baki daya. A saboda haka, akwai bukatar kowanne yaro ya halarci makaranta domin ya samu ilimi," a cewarsa

Mist Hawakins ya cigaba da cewa, "bawa yara ilimi zai taimaki dukkan nahiyar Afrika ba iya Najeriya da ke da kabilu da dama ba.

"Hakan ne yasa dole mu hada karfi da karfe domin inganta rayuwar yara, wadanda su ne kasa zata dogara da su a nan gaba."

Ya kara da cewa makasudin shirya taron shine domin bullo da wasu hanyoyi a jihohin arewa da zasu tabbatar yara a yankin sun samu damar halaratar makaranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel