Anyi ba ai ba: Wata 'yar madigo ta kashe kanta saboda abokiyar iskancinta ta mutu

Anyi ba ai ba: Wata 'yar madigo ta kashe kanta saboda abokiyar iskancinta ta mutu

- Wata budurwa ta kashe kanta bayan mutuwar wata kawarta da suke aikata madigo tare

- An bayyana cewa budurwar ta kasa jure rashin masoyiyar tata, inda ta dinga wallafa rubutu kala-kala akan yadda take ji saboda rashin kawarta

- A karshe an bayyana cewa an samu gawarta a kusa da wata gada yayin da ta hau ta fado

Wata budurwar da aka bayyana sunanta da Jay Dor ta kashe kanta bayan mutuwar kawarta wacce suke aikata madigo tare mai suna Giovanni Doll.

An iske Doll a mace ne bayan ta kwanta bacci, amma kuma dama dai tana fama da rashin lafiya na ciwon daji, inda ita kuma Jay Dor ta kashe kanta saboda bakin cikin mutuwar kawarta ta.

KU KARANTA: Kwadayi mabudin wahala: Wata karuwa ta yiwa wani dan sanda tofin Allah tsine a cikin jama'a bayan yayi lalata da ita ya hanata kudinta

Lamarin ya samo asali ne tun lokacin da Doll ta mutu, ida ita kuma Jay Dor ta kasa jurewa ta dinga zuwa shafin Facebook tana rubutu akan cewa za ta kashe kanta.

Daga baya sai ake samun labari cewa ta kashe kanta yayin da ta hau wata gada mai tsawo ta fado.

Amma kuma kafin ta kashe kan nata ta nemi gafarar mutane su yafe mata, inda ta ce ta riga ta yiwa masoyiyar tata alkawarin za ta bita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel