An yi ram da Saurayin da ya ke lalata kananan yara a Jihar Neja

An yi ram da Saurayin da ya ke lalata kananan yara a Jihar Neja

Mun ji cewa an yankewa wani Mutumi mai suna Abdullahi Abubakar hukuncin dauri a gidan yari na shekaru 7 saboda kwanciya da kananan yara. Wannan abu ya faru ne a Garin Kontagora.

Ko da a ka karantowa Matashin laifuffukansa, sai ya amince da cewa duk ya aikata, ya kuma nemi afuwa. An yanke masa daurin shekaru 7 da damar beli bayan ya yi shekaru 4 a kurkuku.

Dakarun hukumar Hisbah na Kontogora ne su ka kai Abdullahi Abubakar mai shekara 33 kara gaban ‘yan sanda a Ranar 22 ga Watan Yuli, 2019, da zargin laifin lalata wasu Almajirai har 32.

Jagoran Dakarun Hisbah na Garin Kontogora, Murtala Abdullahi, shi ne ya kai karar wannan Matashi bayan da wasu Yara da ke karatu su ka koka da cewa Abdullahi ya na kwanciya da su.

KU KARANTA: ‘Yan Sanda sun bayyana shirin da su ke yi na ceto 'Dan adawan da a ka sace a Kaduna

Wannan abu ya fari ne a Unguwar Sabon-Gari da ke cikin karamar hukumar Kontogora a jihar Neja. A Ranar Lahadin nan ne jami’an ‘yan sanda su ka shirya, su ka kama wannan Mutumi.

A na zargin cewa Abdullahi Abubakar ya dade ya na aikata wannan barna da kananan yara. Da a ka tasa shi a gaba da tambayoyi, Abdullahi ya shaidawa ‘yan sanda cewa ya kan sadu da yaran.

Abdullahi ya bayyana cewa ya kan cirewa yaran masu karatu wando ne a lokacin da su ke tsakar barci, a haka ya ke kokarin tarawa da su. Abdullahi ya ce ya sadu da Almajirai akalla 32 a Garin.

Abdullahi Abubakar ya fadawa jami’an tsaro cewa bai san abin da ya hau kansa da ya rika kwanciya da kananan yaran ba. Wannan Matashi ya ce sharrin shaidan ne ya rutsa da shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel