Bata-gari su na rabawa mutane aikin karya da sunan Gwamna a Jihar Imo
Mun ji cewa Mai girma gwamnan jihar Imo, Rt. Hon. Emeka Ihedioha, ya jawo hankalin jama’a su buda idanunsa radau domin akwai masu bin gari su na damfarar Bayin Allah da sunansa.
Kamar yadda labari ya zo mana a farkon makon nan, gwamna Emeka Ihedioha ya jawo hankalin mutanen jihar Imo cewa ka da su burma hannun ‘yan damfara masu ikirarin raba ayyukan bogi.
Mai girma Emeka Ihedioha ya yi wa jama’an jihar Imo da ya ke mulka karin haske ne ta bakin babban Sakatarensa na yada labarai watau Chibuike Onyeukwu a Ranar 4 ga Watan Agusta, 2019.
Jawabin da Mista Chibuike Onyeukwu ya fitar ya nuna cewa, wadannan mutane su na yawo su na saida fam na aikin shirin nan na Sustainable Development Goals watau SDG a kan kudi N125, 000.
KU KARANTA: APC: Gwamnan Kogi zai yi watsi da Mataimakinsa a zaben 2019
Tuni wadannan Miyagun mutane sun bude asusun a banki da shafukan bogi na damfarar mutane a kafafen yada labarai na zamani irin su Facebook da WhatsApp da sunan Gwamnan Imo.
Onyeukwu ya bayyana cewa wadannan mutane su na kokarin batawa mai girma gwamna Emeka Ihedioha suna ne da kuma gwamnatinsa. A Mayun bana ne Ihedioha ya dare kan mulki a PDP.
Shirin na SDG ya na cikin manyan tsare-tsaren majalisar dinkin Duniya. Kila wannan ya sa ‘yan damfarar ke kokarin ci da sunan gwamnan ta hanyar karbar kudin bada aikin bogi daga jama’a.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng