Tanimu Akawu ya musanta zargin Hadiza Gabon da Maryma Yahaya da karuwanci

Tanimu Akawu ya musanta zargin Hadiza Gabon da Maryma Yahaya da karuwanci

Fitaccen jarumin fina finan Kannywood, Tanimu Akawu wanda a baya sunansa ya yi ta yawo a kafafen sadarwar zamani inda aka ruwaito cewa wai ya zargi matan Fim da bin maza masu kudi domin samun kudi, ya musanta wannan zargi.

A wancan rahoto, an ruwaito Akawu ya ambaci sunayen wasu fitattun jarumai mara biyu da suka hada da Hadiza Gabon da Maryam Yahaya, inda har aka ce ya yi misali da wayoyin hannun Maryam, da kuma motar Gabon, da cewa ko shi da ya dade yana Fim ba zai iya saya ba.

KU KARANTA: Rundunar Yansanda ta saki lambobin wayoyin masu magana da yawunta na jahohi 36

Sai dai Akawu ya musanta wadannan zarge zarge gaba daya, inda yace kazafi, sharri da karya kawai ake yi masa, Akawu ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Aminiya, inda yace tabbas ya gabatar da hirar da ake magana da Human Right Radio, bai fadi ambaci sunan kowacce yar Fim ba, balle ya kirata karuwa.

“A gaskiya ba ni ba ne, na yi bakin ciki da wannan labari, a zaharin gaskiya kimanin wata bakwai da ta wuce na yi hira da gidan rediyo na Human Rights da ke Abuja, an nadi muryata, an kuma dauke ni a bidiyo, babu wurin da na kira sunan Hadiza Gabon ko Maryam Yahaya sannan na kira su da sunan karuwai.

“Hadiza Gabon ta kira abokin aikina Al’Amin Buhari kasancewar ba ta da lambata, ni ma ba ni da tata, Al’Amin ya sanar da ita ba abin da na fada ba ke nan. Na samu labarin ma ta yi ikrarin kai ni kara, amma ta je gidan rediyon Human Rights din ta gane ba abin da na fada ba ke nan.

“An tambaye ni ko me ya sa mata ’yan fim suka fi maza kudi da famtamawa, sai na ce dole su fi mu, domin suna yin kwalliya, kuma suna da samari masu kudi da za su ba su kudi, mu kuma maza ba a ba mu. Amma ban ambaci sunan kowa ba. An tambaye ni ko ta yaya suke samun kudi, na ce wa mai tambayar ya je ya tambaye su.” Inji shi.

Akawu yace bai taba ganin Maryam Yahaya ido da ido ba, amma Hadiza ta taba taimakonsa har ya samu tallar Indomie kuma ya samu kudi, don haka bai ga dalilin da zai yi mata haka ba. Daga karshe ya yi alkawarin daukan matakin shari’a a kan duk wadanda suka aikata masa wannan cin mutunci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel