Kwadayi mabudin wahala: Wata karuwa ta yiwa wani dan sanda tofin Allah tsine a cikin jama'a bayan yayi lalata da ita ya hanata kudinta

Kwadayi mabudin wahala: Wata karuwa ta yiwa wani dan sanda tofin Allah tsine a cikin jama'a bayan yayi lalata da ita ya hanata kudinta

- Wata karuwa ta tonawa wani dan sanda asiri a cikin bainar jama'a bayan yayi zina da ita ya hanata kudinta

- Karuwar wacce ta bayyana cewa sunyi yarjejeniya da dan sandan akan zai bata dubu bakwai idan ta kwana dashi, a karshe ya dauki dubu hudu ya bata

- Wannan lamari dai yasa mutane suka taru akan dan sandan da karuwar, inda dakyar aka samu aka raba rikicin

Wani jami'in dan sanda da ba a bayyana sunanshi ba ya debo ruwan dafa kansa, yayin da wata karuwa da yayi lalata da ita ya hanata kudinta ta ci masa mutunci a cikin bainar jama'a a jihar Legas.

Dan sandan sunyi yarjejeniya da karuwar akan zai biyata naira dubu bakwai idan ta kwana da shi, amma da safe sai ya dauki dubu hudu ya bata, hakan ya jawo masa wannan tonon silili.

KU KARANTA: Tirkashi: Abinda zamu yiwa masu kokarin juyin mulki a kasar nan - Shugaban hukumar 'yan sanda yayi gargadi

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonshi ya wallafa lamarin a shafinsa na Facebook, inda ya ce:

"Dan sandan ya dauki karuwar zuwa gidansa idan ya amince zai bata naira dubu bakwai idan ta kwana dashi, amma sai lamarin ya canja da safen nan, inda yaki bata ko sisi ya dauki dubu daya ya bata akan ta biya kudin masu daki.

"Ni da kaina sai dana yiwa dan sandan magana, ganin kayan dake jikinsa da kuma yanayin shekarunsa, amma ina bai kulani ba, sai da muka kwace hularsa da fitilarsa, daga nan ne ya cire dubu hudu ya bai wa yarinyar. Wannan lamari ya faru yau da safe a Idasho yankin Lekki dake jihar Legas."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel