Sanata Kalu Ya Sha Rubdugu saboda Yabon Shugaba Tinubu

Sanata Kalu Ya Sha Rubdugu saboda Yabon Shugaba Tinubu

  • Jam’iyyar NDC ta yi wa Sanata Orji Uzor Kalu rubdugu kan yabon da ya yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu game da halin tattali arziki
  • A bayanin da ya yi, Kalu ya nuna cewa shugaba Tinubu ya yi ayyuka masu kyau a Najeriya kuma hakan zai saka 'yan kasa su zabe shi
  • Sai dai NDC ta masa kakkausan martani, inda ta ce maganganun Sanatan ba daidai ba ne domin a cewarta 'yan Najeriya na shan wahala

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar NDC ta soki babban mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, kan kalaman da ya yi na yabon gyaran tattalin arzikin shugaba Bola Tinubu.

A martanin da NDC ta yi, ta ce kalaman Sanatan na yaudara ne kuma ba su dace da halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba na wahalhalun rayuwa.

Kara karanta wannan

Duk da rasa kujerarsa, tsohon minista ya ba da mamaki kan magana game da Tinubu

Sanata Orji Uzor Kalu
Sanata Orji Kalu a zauren Majalisar dattawa. Hoto: Sanator Orji Uzor Kalu
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa Mataimakin sakataren yada labarai na na jam’iyyar, Abdulmumin Abdulsalam, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a Abuja.

Kalaman Orji Kalu kan Bola Tinubu

Kalu ya bayyana cewa yana da yakinin cewa Tinubu zai ci gaba da zama wanda ba za a iya kayar da shi ba a zaben 2027, duk da kokarin ‘yan adawa na hada kai a ADC.

Dangane da tattalin arziki, tsohon gwamnan jihar Abia ya ce akwai cigaba da aka samu, amma har yanzu akwai kalubale kadan, yana mai cewa gyare-gyaren na bukatar lokaci kafin su fara tasiri.

Business Day ta rahoto ya ce:

“An samu cigaba a matakin kasa, tare da karuwar amincewar masu zuba jari, amma har yanzu akwai matsaloli. Gyaran tattalin arziki yana daukar lokaci,”

In ji shi.

Jam'iyyar NDC ta yi Allah-wadai da Kalu

Sai dai NDC ta yi watsi da wannan ra’ayi na Kalu, tare da mayar da martani mai tsauri, Abdulsalam ya jaddada cewa karfin jam’iyyun adawa na karuwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gumi ya magantu kan 'yan bindiga da sojojin Turkiyya ke shirin zuwa Najeriya

Ya ce:

“Muna Allah-wadai da Sanatan mai wakiltar Abia ta Arewa kan kalamansa masu rudani game da halin da kasa ke ciki da kuma matsayin jam’iyyun adawa a Najeriya.
“Muna kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa karfin hadin kan siyasa da ‘yan adawa ke ginawa zai kayar da jam’iyyar da ke mulki wadda ke kokarin lalata dimokuradiyya ta hanyar mamaye gwamnati, amfani da talauci a matsayin makami, da kuma takura wa ‘yan adawa.”

Jam’iyyar ta kara da cewa yabon da Kalu ya yi wa manufofin tattalin arzikin shugaban kasa ba ya nuna gaskiyar halin da ake ciki.

Shugaba Bola Tinubu a jihar Katsina
Lokacin da Bola Tinubu ya kai ziyara jihar Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

An ruguza allunan Shugaba Bola Tinubu

A wani labarin, mun kawo muku cewa ana zargin wasu matasa sun ruguza allunan da aka kafa a jihar Ondo domin tallata shugaba Bola Tinubu a Ondo.

Wata kungiyar jam'iyyar APC ta bayyana cewa za ta dauki mataki a kan masu lalata allunan domin hakan ya saba dokar kasa kan siyasa.

Baya ga haka, kungiyar ta bukaci jami'an tsaro su tabbatar da sun hukunta duk da aka samu da laifin lalata allunan a fadin jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng