Zargin Madigo: Sabon rikici ya barke tsakanin Sadiya Kabala da Jakadiyar Tonon Asiri

Zargin Madigo: Sabon rikici ya barke tsakanin Sadiya Kabala da Jakadiyar Tonon Asiri

- Wani sabon rikici ya barke tsakanin jaruma Sadiya Kabala da Jakadiyar Tona Asiri wacce ta yi kaurin suna a shafin sada zumunta na Instagram

- Jakadiyar dai ta sanya wani hoton jaruman biyu Sadiya Kabala da Maryam Yahaya, ta kuma bayyana cewa yadda suka tsaya kusa da juna bai kamata ba domin mutana za su iya zargin su

- Wannan dalilin ne yasa jaruma Sadiya Kabala ta dinga aikawa da Jakadiyar sakon zagi kala-kala

Wata sabuwar rigima ta barke tsakanin jaruma Sadiya Kabala da wata mai tonon asiri a shafin Instagram mai suna Jakadiyar Tona Asiri.

Da farko dai Jakadiya ce ta fara wallafa hoton Sadiya Kabala wanda ta dauka tare da jaruma Maryam Yahaya, sannan sai Jakadiyar ta ce:

"Cabdijam, wato Maryam da kuma Sadiya irin wannan hoto haka, ai sai ku shiga zargi, ga hammatarki duk tayi gumi ya kamata a rika saka hijabi. Allah ya shirya."

KU KARANTA:

Abinda wannan mata ke nufi shine, ganin yadda suka dauki hoton kusa da kusa yasa take ganin za a iya yi musu zargin madigo.

Wannan magana da Jakadiya ta yi ba ta yiwa Sadiya Kabala dadi ba, inda ta shiga bangaren da ake mayar da martani ta dinga surfawa Jakadiyar zagi.

Mutane da yawa suna ganin wannan abu da Jakadiyar ta yi bai kamata ba, tunda hoto dai irin wannan ba yanzu ne aka fara daukar shi ba, bai kamata ta sako maganar madigo a zancenta ba.

Za dai mu cigaba da bibiyar lamarin muji yadda za ta kasance tsakaninsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel