Latest
Rundunar Yansandan Najeriya ta saki jerin lambobin wayoyin jami’an hulda da jama’a na rundunar dake dukkanin jahohin Najeriya 36 tare da babban birnin tarayya Abuja domin kai rahoto kai tsaye ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana abin da ya ware domin aikin RUGA. Ita Enang ya ce Gwamnatin nan ta kasafta Biliyan 2.2 domin aikin RUGA a fadin Najeriya a wannan shekara ta 2019.
Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun kai wani samame gidan tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari, dake garin Talatar Mafara domin gudanar da bincike.
Mun kawo maku abin da Olusegun Obasanjo ya fada bayan ya gana da Fulani. Za ku ji batutuwan da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya yi magana a kai a lokacin da a ka yi wani zama jiya.
Kungiyar Najeriya a kasar Afirka ta Kudu, a ranar Lahadi ta bayar da tabbacin yadda ajali ya yi wa wani mai shekaru 43 shiga wuri, Benjamin Okoronkwo, direban motar tasi dan asalin garin Okposi da ke karamar hukumar Ohaozara.
A ranar Asabar kasar Nijar ta yi bikin cika shekaru 59 da samun 'yancin kai daga hannun kasar Faransa wadda ta yi maya mulkin mallaka. Bikin a wannan karo na zuwa ne daidai da lokacin da matsalolin tsaro suka dabaibaye kasar.
A ranar Laraba, 17 ga watan Yuli, ne rundunar 'yan sanda ta sanar da dokar hana duk wata zanga-zanga a cikin Abuja domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al'umma. An saka dokar ne biyo bayan gumurzun da aka sha tsakanin jami'a
A cewar wata majiyar, matar magidancin ce ta sanar da shi cewa ita da kaninsa, Pius, suna kwana tare. Shi kuma magidancin ya dauki bindiga cikin fushi ya nufi gidan surukin kanin nasa, inda bayan cacar baki ya harbe shi. Rahotanni
Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a yayin babban zabe da aka gudanar a watan Fabraitun 2019, Atiku Abubakar, a ranar Asabar ya ce gwamnatin shugaban kaasa Muhammadu Buhari ta riga ta gama yiwa Najeriya lalata.
Masu zafi
Samu kari