An harbe dan Najeriya murus a kasar Afirka ta Kudu

An harbe dan Najeriya murus a kasar Afirka ta Kudu

Kungiyar Najeriya a kasar Afirka ta Kudu, a ranar Lahadi ta bayar da tabbacin yadda ajali ya yi wa wani mai shekaru 43 shiga wuri, Benjamin Okoronkwo, direban motar tasi dan asalin garin Okposi da ke karamar hukumar Ohaozara ta jihar Ebonyi.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta gabatar da sanadin mai magana da yawunta, Mista Ikele Odefa, ya ce an harbe Benjamin da misalin karfe 3.00 na daren ranar Asabar, 3 ga watan Agusta cikin motarsa ta neman kudi.

A wani rahoto da kungiyar ta aike da shi zuwa kamfanin dillancin labarai na kasa, ta ce tunin hukumar 'yan sandan kasar Afirka a ofishin ta na Mofartview da ke birnin Johannesburg ta fara gudanar da bincike a kan wannan mummunar aika-aika.

Mista Odefa ya ce da ya ke dai mutuwa ba ta barin wani domin wani yaji dadi, marigayi Benjamin ya mutu ya bar 'ya'ya biyu da kuma matar sa daya.

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, an burmawa wasu 'yan Najeriya biyu wuka a ciki murus har lahira a ranakun 5 da kuma 6 ga watan Afrilun 2019 cikin birnin Johannesburg a kasar Afirka ta Kudu.

KARANTA KUMA: Jamhuriyyar Nijar ta cika shekara 59 da samun 'yancin kai

Ana iya tuna cewa, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya ce gwamnatin kasar nan ba za ta ci gaba zuba idanu a kan yadda ake yiwa 'yan Najeriya dauki dai-dai a kasar Afirka ta Yamma.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel