Neja da Jihohin Arewa 10 Za Su Fuskanci Iska Mai Karfi da Ruwan Sama Gobe Juma'a
- Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu yanayin zafi da rana a gobe Juma'a, amma za a samu ruwan sama da iska a wasu jihohin Arewa
- Wasu jihohin Arewa da Kudancin ƙasar za su fuskanci iska mai karfi da kuma ruwan sama mai yawa, tun daga safiya har zuwa yammacin ranar
- NiMet ta buƙaci matafiya da direbobi da su kasance masu taka-tsantsan yayin tuki domin guje wa haɗurran da santsin titi ke yawan haddasawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Juma'a, 17 ga watan Afrilu, 2026, inda ta ce akwai yiwuwar samun iska mai karfi da ruwan sama a sassa daban-daban na ƙasar.
Hukumar ta buƙaci ƴan Najeriya da su kasance cikin shiri domin kiyaye afkuwar haɗurra sakamakon sauyin yanayin da za a fuskanta.

Kara karanta wannan
Yakin Iran, Amurka: Najeriya da wasu kasashe na iya samun tallafin dala biliyan 50

Source: Facebook
Hasashen yanayin Juma'a a jihohin Arewa
A yankin Arewa, ana ran samun yanayin zafi da rana, amma za a samu haduwar hadari a wasu wurare da safe. Ana kuma sa ran samun ruwan sama da tsawa a jihar Taraba, kamar yadda NiMet ta wallafa a shafinta na X.
Da yammacin ranar Juma'a, ana sa ran ruwa mai matsakaicin ƙarfi zai sauka a jihohin Bauchi, Gombe, Kaduna, Adamawa, da kuma Taraba.
Rahoton NiMet ya nuna cewa wadannan jihohi za su fuskanci iska mai ƙarfi da walƙiya yayin da ake sheka masu ruwan sama.
A Arewa ta Tsakiya kuwa, za a tashi da hadari da safe musamman a jihohin Neja da Nasarawa. Zuwa yamma, ana sa ran samun ruwan sama a Abuja, da jihohin Kwara, Benue, Plateau, Kogi, Neja da Nasarawa.
Hasashen yanayi a jihohin Kudu
Yankunan Kudancin Najeriya za su kasance cikin yanayin hadari tun da safe, tare da yiwuwar samun ruwan sama a jihohin Rivers, Bayelsa, Cross River, da Akwa Ibom.
Zuwa yamma kuwa, ruwan saman zai sauka a kusan dukkan jihohin yankin ciki har da Oyo, Ebonyi, Enugu, Abia, Osun, Ekiti, Anambra, Ondo, Ogun, Edo, Imo, Delta, Bayelsa, Rivers, Lagos, Cross River da Akwa Ibom.

Source: Facebook
Shawarwarin NiMet ga mutane
Hukumar ta fitar da muhimman shawarwari ga jama'a kamar haka:
- Mutane su yi nesa nesa da wuraren da ambaliya ke shafa yayin da ake ruwa.
- Direbobi su rage gudu sakamakon rashin gani sosai da kuma santsin hanya.
- A nemi wurin buya idan ana tsawa domin kariya daga saukar walƙiya.
- Sannan kamfanonin jiragen sama su rika samun rahoton yanayi daga NiMet domin tabbatar da tsaron jirage yayin tashi ko sauka.
Karanta rahoton NiMet a nan kasa:
Jihohi 33 za su fuskanci ambaliya a 2026
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamanti ta sanar da cewa garuruwa 14,118 a ƙananan hukumomi 266 za su fuskanci barazanar ambaliya.
Jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya Abuja ne aka yi hasashen cewa ambaliyar za ta shafa tsakanin watan Afrilu zuwa Nuwamba, 2026.
Manyan birane kamar Legas, Kano, Abuja, da Kaduna za su fuskanci ambaliya mai tsanani sakamakon toshewar magudanun ruwa a jihohinsu.
Asali: Legit.ng
