Shugaba China Ya ba Trump Amsa 'Mai Kyau' yayin da Ya Nemi a Daina Tura Makamai Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya lallaba kasar China kuma ba za ta tura makamai don taimakawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba
- Donald Trump ya ce ya rubuta wasika ga shugaban China, Xi Jinping kuma ya dawo masa da amsa kan batun turawa Iran makamai
- Wannan na zuwa ne bayan jita-jita ta yi yawa cewa kasar China za ta tura karin makami Iran, lamarin da Amurka ta nuna ba ta ji dadi ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ya tuntubi gwamnatin kasar China kan zargin da ake yadawa cewa za ta bai wa Iran tallafin makamai.
Shugaba Trump ya ce ya roki China da kada ta turawa Iran karin makamai, kuma Shugaban kasar, Xi Jinping ya tabbatar masa da cewa hakan ba za ta faru ba.

Kara karanta wannan
China ta dura kan Amurka, ta yi magana mai zafi kan zargin tura makamai zuwa Iran

Source: Getty Images
Donald Trump ya lallaba China kan taimakon Iran
Tashar NBC News ta rahoto cewa Trump ya bayyana haka ne a wasu sakonni da ya fitar yau Laraba, 15 ga watan Afrilun 2025.
“Na ji labarin cewa kasar China tana tura wa Iran maiamai, ina tunanin kun ga labarin, ya karade ko'ina."
“Hakan ya sa na rubuta masa (Shugaban kasar China) wasika ina neman sa da ya daina yin hakan, shi kuma ya rubuto mani amsar cewa, a takaice dai, ba ya yin hakan.”
Shugaban Amurka ya kuma bayyana cewa kasar China na matukar farin ciki da matakin da ya dauka na bude mashigar Strait of Hormuz, duk da ci gaba da takaddama a yankin.
Trump ya cika baki kan mashigar Hormuz
Trump ya ce matakin da ya dauka ba wai domin Amurka kadai ba ne, har ma domin kasashen duniya baki daya, ciki har da China.
“China na matukar farin ciki da na bude mashigar Hormuz gaba daya. Ina yin hakan ne domin su da kuma duniya baki daya.

Kara karanta wannan
Ana batun sulhu da Iran, Shugaban Amurka zai ballo yakin da zai jefa kasashe a bala'i
'Wannan yanayi ba zai sake faruwa ba har abada kuma sun amince ba za su tura makamai zuwa Iran ba. Shugaba Xi zai rungume ni sosai idan na isa can nan da ‘yan makonni kalilan," in ji Trump.
Shugaban Amurka zai ziyarci China
Trump ya kuma bayyana cewa yana sa ran ganawa da shugaban China, Xi Jinping, cikin makonni masu zuwa, inda ya ce yana fatan zai karbe shi cikin farin ciki.
“Za mu yi aiki tare cikin hikima kuma cikin kyakkyawan yanayi. Shin wannan ba ya fi fada ba?” in ji shi.

Source: Getty Images
Sai dai ya yi gargadi cewa duk da haka, Amurka na da karfin fada idan bukatar hakan ta taso, kamar yadda tashar Al-jazeera ta ruwaito.
A halin yanzu, rahotanni na nuna cewa zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz na ci gaba da tangal-tangal, yayin da Amurka ta kakaba takunkumi kan tashoshin jiragen ruwa na Iran.
China ta nemi a sulhunta Amurka da Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin kasar China ta yi magana kan tashi zaman tattaunawar Islamabad tsakanin Amurka da Iran ba tare da cimma matsaya ba.
China ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran na cikin wani yanayi mai rauni matuka, kuma bai kamata a bari ta rushe ba.
Ta kuma yi kira ga kasashen duniya su tashi tsaye wajen hana duk wani mataki da zai iya jawo sake barkewar yaki tsakanin wadannan kasashe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng