Yakin Iran, Amurka: Najeriya da Wasu Kasashe na iya Samun Tallafin Dala Biliyan 50

Yakin Iran, Amurka: Najeriya da Wasu Kasashe na iya Samun Tallafin Dala Biliyan 50

  • Hukumar IMF na shirin bai wa ƙasashe masu rauni tallafin dalar Amurka biliyan 50 domin rage raɗadin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya jawo
  • Hukumar ta gargaɗi Najeriya da sauran ƙasashe masu fitar da mai da su yi amfani da ƙarin kuɗin shiga wajen biyan bashi da gina al'ummarsu
  • IMF ta kuma jaddada cewa babban burin wannan tallafin shi ne kare talakawa daga matsin rayuwa da kuma tunkarar matsalar ƙarancin abinci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka – Sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya da ya girgiza kasuwannin duniya, asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya nuna alamun ba Najeriya da wasu ƙasashe tallafin kusan dalar Amurka biliyan 50.

Za a bada tallafin ne don taimaka wa ƙasashen wajen jure matsin lambar da yakin ya haifar, musamman ga ƙasashen da suka dogara da shigo da makamashi daga ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan neman dawo da tallafin man fetur

Hukumar IMF na duba yiwuwar bada tallafin $50bn ga Najeriya da wasu kasashe
Hagu zuwa dama: Jose Luis De Haro, jami'in sadarwa na IMF; Pierre-Olivier Gourinchas, daraktan IMF; Petya Brooks, mataimakiyar Gourinchas da Deniz Igan, a taron IMF a Amurka. Hoto: Kent NISHIMURA
Source: Getty Images

Najeriya na iya samun tallafin $50bn

Shugabar hukumar IMF, Kristalina Georgieva, ce ta bayyana hakan a yau Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026, yayin taron hadin gwiwa tsakanin IMF da Bankin Duniya da ke gudana a birnin Washington DC, in ji rahoton Leadership.

Georgieva ta bayyana cewa rikicin ya haifar da abin da ta kira "matsin lamba mara misaltuwa," wanda ya fi shafar ƙasashen da ba su da isasshen tanadin kuɗi.

A cewarta, ƙasashe aƙalla guda 12 ne za su buƙaci tallafin kuɗi tsakanin dalar Amurka biliyan 20 zuwa biliyan 50 a cikin ɗan kankanin lokaci, kuma mafi yawan waɗannan ƙasashe sun fito daga yankin Afirka ne.

Shugabar ta jaddada cewa kofar IMF a bude take ga kowace ƙasa da ta nemi tallafi domin kare tattalin arzikinta da kuma kare talakawa daga matsin rayuwa.

IMF ta gargadi kasashe kan cin bashi

Ta ƙara da cewa tattaunawar da ake yi a taron na Washington na mayar da hankali ne wajen gano ƙasashen da rikicin ya fi shafa domin samar musu da tallafin da ya dace.

Kara karanta wannan

An gano kasar da ta ba Iran babbar gudunmawa a kai hare hare kan sojojin Amurka

Game da manufofin tattalin arziki, Georgieva ta gargaɗi ƙasashe game da yawan karbar basussuka, tana mai cewa bashin duniya na iya wuce kashi 100 na jimillar arzikin duniya (GDP) nan da shekarar 2029.

Ta buƙaci gwamnatocin kasashe, musamman wadanda ke kokarin farfado da tattalin arzikinsu, da su yi hattara kan sha'anin bashi da kuma mayar da hankali kan tallafa wa talakawa.

IMF ta ce tana ci gaba da aiki da Bankin Duniya da sauran abokan hulɗa domin tabbatar da cewa rikicin Gabas ta Tsakiya bai jefa tattalin arzikin duniya cikin babbar koma-baya ba.

IMF ta gargadi Najeriya kan ciwo bashin da ba za ta iya biya a kan lokaci ba.
Shugabar IMF, Kristalina Georgieva na jawabi a taron IMF da Bankin Duniya a Washington, DC, a ranar 15 ga Afrilu, 2026. Hoto: Kent NISHIMURA / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Yadda yakin Iran zai shafi Najeriya

A ɓangare guda, wani babban jami'in IMF, Davide Furceri, ya yi tsokaci kan yadda rikicin zai shafi Najeriya, a cewar rahoton The Cable.

Ya bayyana cewa, Najeriya a matsayinta na mai fitar da man fetur, na iya samun ƙarin kuɗaɗen shiga sakamakon hauhawar farashin danyen mai a duniya.

Furceri ya yi gargaɗin cewa bai kamata Najeriya ta yi almubazzaranci da waɗannan ƙarin kuɗaɗen ba; kamata ya yi ta yi amfani da su wajen biyan bashi da kuma gina tanadin kuɗi na nan gaba.

Kara karanta wannan

'Sai dai a mutu,' Kasar Cuba ta daina jin tsoron Trump, ta shirya yaki da Amurka

Ya kuma yi gargaɗin cewa tsadar taki, sufuri, da makamashi na iya shafar harkar noma da kuma haifar da matsalar ƙarancin abinci a ƙasashe masu rauni.

Lauya ya fadi illar IMF ga Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, babban lauya, Femi Falana, SAN, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan cire tallafin ma ida ya yi a farkon mulkinsa.

Ya ce cire tallafin mai yana da alaƙa da tsare-tsaren IMF da Bankin Duniya da suka daɗe suna shirya wa ƙasashe masu tasowa, wadanda ke jefa mutane a talauci.

Falana ya zargi asusun bada lamuni na IMF da Bankin Duniya da yi wa tattalin arzikin Najeriya mugun kulli, ciki har da kitsa cire tallafin da kuma karya darajar Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com