An Fara Matsa wa Tinubu daga Amurka, Ana Son Ya Kori Matawalle daga Kujerar Minista
- Yar majalisar jihar Florida, Kimberly Daniels, ta tsoma baki a cikin al'amarin tsaron Najeriya tare da ba Bola Tinubu shawara
- Wani rahoton tsaro da ta gabatar ya nuna karuwar hare-hare a lokacin bukukuwan Easter a jihohin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma
- Ms. Daniels ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya duba shugabancin tsaro tare da ɗaukar mataki a kan Bello Matawalle
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
USA – Wata ‘yar majalisar dokoki ta jihar Florida a Amurka, Kimberly Daniels, wace ita ce shugabar kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya ta cire ko ta sauya Bello Matawalle daga mukaminsa na Karamin ministan tsaro.
Kimberly Daniels ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, 2026 yayin gabatar da wani rahoto kan matsalar tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan
"Duk na kere su": Atiku ya kwatanta farin jininsa da na Kwankwaso, Tambuwal a Arewa

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa rahoton da aka gabatar ya fi mayar da hankali a kan kashe-kashen da aka samu a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.
An yi nazari kan tsarin Najeriya a Amurka
Ita kuwa Leadership ta wallafa cewa rahoton ya yi nazari kan yadda shugabancin tsaro ke aiki, musamman bayan hare-haren da suka faru a lokacin bukukuwan Easter na shekarar 2026.
Ta ce shugabannin al’umma da wadanda suka tsira sun koka da cewa akwai babban gibi tsakanin kalaman gwamnati da ainihin halin tsaro a kasa kamar yadda ya ke shafar su.
Rahoton ya kuma nuna damuwa kan ci gaba da rike Bello Matawalle a mukamin, inda aka ambaci wasu “alamun gargadi”, ciki har da zargin alaka da ‘yan bindiga a lokacin da yake gwamnan Zamfara.
Zargin da aka yi wa Bello Matawalle
Yar majalisar dokoki ta jihar Florida a Amurka, Kimberly Daniels ta ce an kuma zargi Matawalle da boye shugabannin ‘yan bindiga, da kuma rashin gogewa a harkar tsaro.
Ms. Daniels ta bukaci a cire ko a sauya Matawalle domin dawo da martabar ma’aikatar tsaro a Najeriya baki daya.
Ta kuma bukaci Bola Ahmed Tinubu ya duba yi duba na tsanaki tare da cire duk wasu da ke kawo barazana ga tsaron kasa.

Source: Original
Ta ce:
"Sakamakon wannan rahoto ya bukaci a yi nazari cikin gaggawa kan shugabanci, daga ciki har da cire ko sauya Minista Bello Matawalle domin dawo da martabar ma’aikatar tsaro.”
Haka kuma, ta ba da shawarar a gudanar da bincike kan zargin hadin kai tsakanin manyan jami’ai da ‘yan bindiga, tare da kara kare al’ummomin da ke cikin hadari.
Ƴar majalisar ta kuma bukaci gwamnatin Amurka da sauran abokan hulda na kasa da kasa su kara matsin lamba na diflomasiyya domin tabbatar da an hukunta duk wadanda ake zargi da taimaka wa ta’addanci.
A cewarta, matsayinta ya samo asali ne daga koken ‘yan Najeriya da suka tuntube ta, inda ta ce kudurin majalisar Florida mai lamba 761 yana goyon bayan sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake damuwa da su.
Trump ya samu goyon bayan Majalisar Amurka
A baya, mun wallafa cewa Majalisar dattawan Amurka ta sake zama a kan kudirin hana Shugaban ƙasar, Donald Trump ci gaba da yaƙi da Iran karo na huɗu.
Sai dai ƙuri’ar ta rabu tsakanin jam’iyyun siyasa, inda mafi yawan ‘yan Republican suka ƙi amincewa da kudirin tare da goyon bayan Trump ya ci gaba da yaƙin.
Amma wadanda suka goyi bayan kudirin sun ce Trump ya wuce makaɗi da rawa a fuskar kundin tsarin mulki, amma magoya bayansa sun kare matakin.
Asali: Legit.ng

