Amurka Ta Samu Alheri Mai Girma a Yaki da Iran, Tana Dab da Kafa Tarihin Yakin Duniya na 2
- Yaki da kasar Musulunci ta Iran ya zama alheri ga kasar Amurka wajen fitar da danyen mai zuwa kasashe daban-daban a duniya
- Alkaluman bincike sun nuna cewa Amurka ta fitar da mai da yawa, wanda ya kai adadin da ba a taba gani ba tun yakin duniya na biyu
- Masana sun bayyana cewa Amurka na dab da kai iyakar ƙarfin da take da shi wajen fitar da mai, wanda ake hasashen zai kai ganga miliyan 6 a rana
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
America - Amurka na dab da zama mai fitar da danyen mai fiye da yadda take shigowa da shi cikin kasar a makon da ya gabata, karon farko tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.
Hakan ta faru ne sakamakon ƙaruwar buƙatar mai daga kasashen Turai da Asiya, wanda ya samo asali daga yakin da ya auku a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Kudurin hana Trump sayar wa Isra'ila bama bamai ya gamu da cikas a majalisar dattawa

Source: Getty Images
Reuters ta ruwaito cewa wannan ci gaba ya biyo bayan rikicin yaƙi tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, wanda ya haifar da matsala mafi girma a tarihin kasuwar makamashi ta duniya.
Barazanar da Iran ta yi kan zirga-zirgar jiragen ruwa ya dakatar da kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur da iskar gas da ke wucewa ta mashigar ruwa ta Strait of Hormuz.
Buƙatar mai ta ƙaru a duniya
Matatun mai a Turai da Asiya, waɗanda ke dogaro da man Gabas ta Tsakiya, sun fara neman mai daga wasu wurare, musamman Amurka, wacce ita ce mafi girma wajen samar da mai a duniya.
Bayanai sun nuna cewa man da ake fitarwa daga Amurka ya kai ganga miliyan 5.2 a kowace rana a makon da ya gabata, mafi girma cikin watanni bakwai, yayin da shigo da shi ya ragu sosai.
Kasashe kamar Netherlands, Japan, Faransa, Jamus da Koriya ta Kudu na daga cikin manyan masu sayen man Amurka, yayin da ta ƙasar Girka ta fara sayen man Amurka a karon farko.
Amurka ta tura mai zuwa Turkiyya
Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa wani jirgi mai ɗauke da ganga 500, 000 na danyen mai na kan hanyarzuwa Turkiyya, wanda zai zama karon farko cikin fiye da shekara guda da Amurka ke fitar da mai zuwa kasar.
Tashin farashin danyen mai na Brent a duniya ya sa man Amurka ya zama mai araha ga masu saye a Turai da Asiya.

Source: Getty Images
A wani lokaci, bambancin farashin ya kai dala 20.69 a kowace ganga, wanda ya sa sayen mai daga Amurka ya fi jan hankali, cewar rahoton The Strait Times.
Bukatar danyen mai na iya wuce karfin Amurka
Masana sun bayyana cewa Amurka na dab da kai iyakar ƙarfin da take da shi wajen fitar da mai, wanda ake hasashen zai kai ganga miliyan shida a rana.
A cewarsu, karuwar fitar da mai na iya fuskantar ƙalubale saboda ƙarancin bututun mai da kuma jiragen ruwa da ake amfani da su wajen jigilar kaya.
Amurka da Iran za su koma teburin sulhu
A wani rahoton, kun ji cewa akwai yiwuwar wakilan kasashen Amurka da Iran su koma ƙasar Pakistan a ƙarshen wannan mako domin ci gaba da tattaunawa.
Majiyoyi sun bayyana cewa za a sake zama domin gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar a birnin Islamabad na kasar Pakistan.
Har yanzu dai babu wani tabbaci daga jami’an Amurka game da wannan shiri, wanda jami’an Iran da na Pakistan suka tattauna a matsayin sirri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

