Ana Shirin Tafiya Hajji, an Fara Barazanar Tsayar da Aiki da Jiragen Sama a Najeriya
- Kamfanonin jiragen sama sun fara barazanar dakatar da aiki yayin da farashin man da suke amfani da shi ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya
- Wasu rahotanni sun nuna cewa farashin man jirgin sama ya tashi da fiye da kashi 300, lamarin da ke cigaba da zama barazana ga 'yan kasuwa
- Tuni dai aka mika takardar gargadi ga ofishin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima da wasu masu ruwa da tsaki kan lamarin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hada-hadar sufurin jiragen sama na dab da tsayawa cak a fadin Najeriya saboda tashin farashin man da suke amfani da shi.
Masu gudanar da kamfanonin jiragen sama sun yi gargadin cewa tashin gwauron zabi da farashin man jiragen sama ya yi ya jefa su a mawuyacin hali, lamarin da ke haddasa fargabar dakatar da zirga-zirgar.

Source: Getty Images
Farashin man jirgi ya tashi a Najeriya
Rahoton Punch ya nuna cewa a karkashin ƙungiyar AON, kamfanonin sun bayyana cewa farashin mai ya karu da fiye da kashi 300 cikin ƙasa da watanni uku.
Sun ce farashin ya tashi daga N900 kan kowace lita a ranar 28 ga Fabrairun 2026 zuwa kusan N3,300 a yanzu, karin da suka bayyana a matsayin “mai tsanani”.
Maganar tsarin kayyade farashi
Kungiyar ta soki tsarin ƙayyade farashin, tana mai cewa bai da wata alaƙa da yadda kasuwar danyen mai ke tafiya a duniya.
AON ta ce:
“Wannan karin farashi mai tsanani da aka ƙirƙira ba ya daidai da karin farashin danyen mai a duniya, wanda ya nuna karin kusan kashi 30 kacal.”
Kamfanonin jiragen saman sun ce sun daure suna aiki duk da karin farashin domin ci gaba da zirga-zirga, amma sun bayyana cewa ƙarfinsu ya kare.
Sun ce:
“Tsawon makonni huɗu da suka gabata, kamfanonin jiragen sama sun ci gaba da aiki saboda kishin ƙasa da kuma hidima ga al’umma. Amma yanzu lamarin ya zama ba za a iya jurewa ba kuma ba mai ɗorewa ba ne.”

Source: Facebook
“A gaskiya, wannan karin farashi marar dalili ya riga ya shafi wani kamfani sosai har ya dakatar da duk ayyukansa tun daga ranar 13 ga Maris, 2026. Hakan na iya faruwa ga sauran kamfanoni idan ba a dauki mataki ba,”
In ji AON.
Jirage za su daina zirga-zirga
Kamfanonin sun kuma bayar da sanarwar cewa idan ba a dauki mataki ba, za su dakatar da ayyukansu daga ranar 20 ga Afrilu, 2026.
Reuters ta rahoto sun ce:
“Saboda haka, muna sanar da cewa idan wannan yanayi ya ci gaba, duk kamfanonin jiragen sama a Najeriya za su dakatar da aiki daga ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2026. Wannan shi ne kira na ƙarshe.”
Magana kan tsadar man fetur
A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan Najeriya sun koka kan yadda farashin man fetur ya tashi a kasar yayin da ake korafi kan man jirgin sama.
Ministan kudi na kasa, Wale Edun ya tabbatar da cewa ana fama da matsalar tsadar man fetur amma hakan ba zai sa a maido da tallafin mai ba.
Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta duba yiwuwar samar da tallafi ga mutane marasa karfi domin rage musu radadin tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng


