Ana Kokarin Sulhu, Amurka Ta Gano Halin da Jagoran Iran, Khamenei Ke ciki bayan Kai Masa Hari

Ana Kokarin Sulhu, Amurka Ta Gano Halin da Jagoran Iran, Khamenei Ke ciki bayan Kai Masa Hari

  • Amurka ta kuma yin ikirarin cewa jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei ya samu munanan raunuka a hare-haren da ta kai masa
  • Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth ya ce wasu rahotanni sun nuna cewa Khamenei ya samu nakasa, amma har yanzu yana raye
  • Wannan kalamai na ministan na zuwa ne yayin da ake tsakiyar kokarin sulhunta Amurka da Iran domin kawo karshen yakin gaba daya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Kasar Amurka ta sake fitowa ta yi ikirarin cewa jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei ya samu raunuka a lokacin yaki.

Wannan ikirari da Amurka ta sake yi na zuwa ne bayan kasashen biyu sun amince da tsagaita wuta na tsawon makonni biyu, kuma sun fara tattaunawar sulhu don kawo karshen yakin gaba daya.

Kara karanta wannan

Iran ta amince da bukatar Amurka, ta canza ahawara kan batun keramakamin nukiliya

Mojtaba.
Jagoran addinin kasar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth ya ce Mojtaba Khamenei, ya samu munanan raunuka sakamakon hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.

Amurka ta fadi halin da Khamenei ke ciki

Hegseth ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da menama labarai a ma'aikatar tsaron Amurka da ke birnin Washington DC yau Alhamis, 16 ga watan Afrilun 2026.

A cewar Hegseth, Mojtaba Khamenei, wanda ya gaji mahaifinsa Ali Khamenei a watan Maris na shekarar 2026, yana raye, amma ya jikkata sosai, har ma ana zargin ya samu nakasa.

Duk da haka, Ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ba ta gabatar da wata hujja kai tsaye da ke tabbatar da wannan iƙirari ba, kamar yadda NBC News ta ruwaito.

Zargin jikkata Mojtaba Khamenei

Rahotannin sun danganta jikkata jagoran Iran da hare-haren sama masu tsanani da Amurka da Isra’ila suka kai kan wasu muhimman wurare, ciki har da inda ake zargin shugabannin Iran ke zama.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaron Amurka ya aika sako mai zafi ga shugabannin Iran

Wasu majiyoyi sun kuma nuna cewa hare-haren sun haddasa mutuwar wasu manyan jami’an gwamnatin Iran, lamarin da ake ganin ya girgiza tsarin shugabanci a ƙasar.

Duk da wannan iƙirari daga bangaren Amurka, gwamnatin Iran ba ta fitar da wani sahihin bayani ko bidiyo da ke nuna halin da Mojtaba Khamenei yake ciki ba.

Abin da aka samu kawai shi ne sanarwa daban-daban daga ofishinsa bayan hawansa kan karagar mulki a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Ministan tsaro.
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth a wurin ajiyar makamai da ke ma'aikatar tsaro a Washington DC Hoto: Pool
Source: Twitter

Wannan lamari na iya ƙara dagula al’amura tsakanin Amurka da Iran, musamman idan aka yi la’akari da cewa yanzu haka suna tattaunawa domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

Amurka ta yi barazanar ci gaba da yakin Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta yi barazanar komawa fagen yaki da kasar Iran matukar tattaunawar sulhun da aka fara ta gaza cimma nasara.

Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce sojojin Amurka sun shirya tsaf domin ci gaba da yakar kasar Musulunci ta Iran idan ta amincewa da batun sulhu.

Ministan ya ƙara da cewa Amurka za ta ci gaba da killace tashohin ruwa na Iran na tsawon lokacin da ya dace, yana nuna cewa babu wani shiri na sassauta wannan mataki a nan kusa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262